Adadin shahidan Lebanon ya kai 3,823 har ila yau lokaci mutane 15,859 ne suka samu raunuka sakamakon wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyuniya ke yi a kasar Labanon.
Hare-haren 'yan sahayoniya a cikin sa'o'i 24 da suka gabata a yankuna daban-daban na wannan kasa sun yi sanadin shahidai 55 da jikkata 160.
Ya kamata a lura da cewa a hukumance an fara tsagaita bude wuta tsakanin kasar Labanon da gwamnatin Sahayoniya da karfe 5:30 na safe agogon Tehran.
Galibin yahudawan sahyoniya suna ganin cewa hukumar Tel Aviv ba za ta iya yin galaba akan Hizbullah ba ne shi yasa ta fake da tsagaita wuta. Sakamakon wani bincike da gidan talabijin na gwamnatin sahyoniyawan ya gudanar ya nuna cewa galibin mahalarta taron sun yi imanin cewa wannan gwamnatin ba ta iya karya lagon Hizbullah ba.
Dubi cikin cikakkun sharuddan yarjejeniyar tsagaita wutar daga mahangar kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya. Kafar yada labaran yahudawan sahyoniya "Khadashut Isra'ila" sun wallafa wasu bayanai a cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin kasar Labanon da gwamnatin sahyoniyawa tare da jera gazawar wannan yarjejeniya ga bangaren yahudawan sahyoniya.
Ganawar da Netanyahu ya yi da shugabannin garuruwan yankin arewa ya ce masu; Mutanen arewa ba za su iya komawa garuruwansu ba.
Firaministan yahudawan sahyoniya ya ce duk da tsagaita bude wuta da aka yi da kasar Labanon, har yanzu mazauna yankin arewacin Palastinu da aka mamaye ba za su iya komawa matsugunan da ke wadannan yankuna ba.
Tashar talabijin ta CNN ta bayyana yanayin wannan taro da zaman dar-dar, inda ta kuma ruwaito cewa wasu daga cikin hakimai da suka hada da magajin garin Kiryat Shmoune da aka mamaye, sun bayyana yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah a matsayin "yarjejeniya ta mika wuya".
Ben Guer shima ya ce: Tsagaita wuta da Lebanon ba za ta mayar da mazauna arewa zuwa ƙasarsu ba
Ministan tsaron cikin gida na gwamnatin sahyoniyawan Itmar Ben Guer ya rubuta a shafinsa na X cewa: Tsagaita bude wuta a kasar Lebanon ba za ta taba mayar da mazauna arewacin kasar zuwa kasarsu ba, kuma ba za ta haifar da da mai ido kan kungiyar Hizbullah ba, amma za mu rasa damar tarihi ta kai masu hari mai tsanani
Ficewar Isra'ila daga Lebanon zai ɗauki kwanaki 60
Wani jami'in gwamnatin Amurka ya shaidawa shafin intanet na Axios cewa: "Yarjejeniyar za ta fara aiki ne a ranar Laraba, kuma dukkan bangarorin za su daina kai hare-hare. Tsarin janyewar sojojin Isra’ila da maye gurbi na sojojin Lebanon zai dauki tsawon kwanaki 60 ba abu ne da za a yi shi cikin dare ba.
Sojojin Isra'ila za su ci gaba da zama a Lebanon har sai an jibge sojojin na Lebanon. Ficewar Isra'ila za ta kasance a sassa daban-daban kuma za a fara aiki a cikin makonni biyu na farko.
Hizbullah ta Iraqi sun yi martini akan wannan tsagaita wuta da cewa: Numfasawar wani yanki na gwagwarmaya ba zai yi tasiri a ayyukan sauran sassan ba.
Kungiyar Hizbullah ta Iraki ta yaba da kuma jaddada tabbatuwarta da gwagwarmayar Lebanon, idan ba gwagwarmaya da sadaukarwar mayakan Hizbullah ba, da ba a cimma nasarar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon ba.
Muna jaddada matsayarmu a fagen gwagwarmayar Palastinu kuma ba za mu taba barin 'yan'uwanmu a Gaza su kadai ba, ba ma ba da wani muhimmanci ga barazanar makiya ba.
Bangare guda kuma mun jiyo martanin masana a Isra’ila inda wani masanin Isra'ila ya tofa albarkacin bakinsa kan tsagaita wuta a Lebanon yana mai cewa ga Netanyaho: Netanyahu, shekara guda Kenan ana kashe mu, ina kuma kake so ka kai mu da tsagaita wuta?!