Kamfanin dillancin labaran
ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya habarta maku cewa: Daya daga cikin
kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya sanar da cewa, wannan
yunkuri na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon yana shirye-shiryen yin yaki na
tsawon lokaci mai tsawo da gwamnatin sahyoniyawa ta hanyar samar da sabbin kwamandojin
sojojinta.
A wata hira da kamfanin dillancin labaran Reuters, wannan kwamandan ya jaddada cewa mayakan Hizbullah sun kafa sabon dakin ayyukan soji na wannan yunkuri bayan shafe sa'o'i 72 na shahadantar da Sayyid Hasan Nasrallah.
A cewar wannan kwamandan
na Hizbullah, sabuwar cibiyar bayar da umarni na ci gaba da aiki duk da
hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a baya, kuma sabuwar rundunar ta Hizbullah tana
aiki ne cikin tsattsar ingantaccen sirri.
Ya yi nuni da cewa:
Mayakan kungiyar Hizbullah suna harba makamai masu linzami da yin yaki ne bisa
umarnin da jagorancin rundunar ta bayar. Har yanzu kungiyar Hizbullah tana da
manyan makamai da suka hada da makamai masu linzami na gaske.
Idan dai ba a manta ba a
yammacin ranar Juma'a 27 ga watan September 2024 ne gwamnatin sahyoniyawan ta
kashe babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Sayyid Hasan Nasrallah ta
hanyar kai hari a unguwar Hara Harik da ke yankin kudancin birnin Beirut babban
birnin kasar Labanon da bama-bamai da gine-gine da dama. Har ila yau, a safiyar
ranar Talata 01 ga watan Oktoban shekarar 2024, sojojin Isra'ila sun sanar da
fara kai farmaki ta kasa a kudancin kasar Lebanon, kan dakarun kungiyar
Hizbullah ta kasar Labanon.