23 Satumba 2024 - 16:33
Ayatullah Sistani Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kawo Ƙarshen Hare-haren Da Gwamnatin Sahyoniyawa Ke Kaiwa Ƙasar Labanon

Ayatullah Sistani Ya Yi Kira Da A Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Ganin An Kawo Ƙarshen Hare-haren Da Gwamnatin Sahyoniyawa Ke Kaiwa Ƙasar Labanon

Babban Marja'in koli Shi'a a kasar Iraki na yi kira ga muminai da su rage wa al'ummar Lebanon wahalhalun da suke sha ta hanyar samar musu da bukatun jin kai da agaji.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait As - ABNA - ya habarta cewa: a cikin wani bayani da ya fitar Ayatullah Sistani babban Marja'i Shi'a na kasar Iraki ya yi ishara da hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ta ke kan kaiwa kasar Labanon inda ya yi kira da a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an dakatar da wadannan hare-hare. hare-hare.

A cikin bayanin da ofishinsa da ke Najaf Ashraf ya fitar, an bayyana cewa, a cikin wannan mawuyacin hali, al'ummar kasar Labanon mai daraja, da ke ci gaba da fuskantar munanan hare-hare da munanan hare-haren gwamnatin sahyoniyawa, ciki har da fashewar wani adadi mai yawa na wayar sadarwar sirri da na'urori da makamantansu, da kuma kai hari ga gidaje da ke cike da jama'a mata da kananan yara da kuma hare-hare da dama a kan kauyuka da garuruwan kudanci da Al-Baqaa, wanda wadannan hare-haren sun yi sanadiyar shahada da raunata dimbin yan gwagwarmaya da jaruman mayaka da sauran fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da kuma hijirar dubun dubatar mazauna daga gidajensu. Marja'in ya nuna goyon bayansa ga masoyan Lebanon masu daraja tare da tausaya musu a cikin wannan babban wahala.

A cikin wannan bayani an ambaci cewa Marja'in koli na addini yana mai mika hannayensa wajen rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kare su da kuma kiyaye su tare da nisantar da su daga sharrin mugaye da azzalumai.

Ayatullahi Sistani ya yi addu'ar samun rahama ga shahidan masu daraja da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

A yayin da yake neman duk wani yunkuri na dakile wadannan hare-hare na dabbanci da kuma kare al'ummar kasar daga mummunan tasirin wadannan hare-hare, ya bukaci muminai da su saukakawa al'ummar Lebanon wahalhalu da suke ciki ta hanyar samar masu da dukkan Abunda suke bukatu na jin kai.

...................................