Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya kawo maku rahoton cewa: a dai dai lokacin zagayowar
ranar 9 ga watan Rabi al-Awwal da kuma zagayowar ranar kama Imamancin Imam
Zaman, Allah ya gaggauta bayyanarsa, wato taron yin mubaya'a da kuma sabunta
alkawari da sojojin kasar Iran suka yi ga Imam Zaman mai taken "Alkwarin Soja"
tare da halartar rundunonin soji, da ma'aikatar tsaro da dakarun kare juyin
juya halin Musulunci a cikin masallacin mai alfarma na Jamkaran tare da gabatar
da jawabin Mai girma kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Sardar
Salami.
















































