Kamfanin dillancin
labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya kawo maku bayani wasu hadisai Bisa dacewa da
ranar shahadar Imam Hasanul Askari As da kuma kamawar Imamancin Imamul Mahdi
Mai Zamani As zamu kawo wa masu bibiyarmu wasu daga cikin hadisai da aka
ruwaito daga ciin littafin Tafsir din Imam wanda ake kira da (Tafsirul Imam
Askari As)
1- Dangane Da Cewa Ayyukan Bayi Ba Sa Karbuwa Sai Suna Da Wilayar A’imma As:
Imam As ya ce: “ Amma ita Zakka hakika manzon Allah (sawa) ya ce: “wanda duk ya bayar da zakka ga wanda ya cancanceta kuma ya tsayar sallah tare da kiyaye iyakokinta’ kuma bai hada su da wasu zunubai da suke lalata su ba’ to zai zo ranar Alkiyama dukkan wanda duk halittar da ke filin nan zai na fatan ya kai matsayinsa, yayin da kamshin Aljana zai daukakasa zuwa mafi daukaka da matsayin dakunanta a kusa da wanda ya shugabantar na daga iyalan Muhammad da iyalansa masu tsarki da tsarkaka.
Wanda kuwa duk yayi rowa yaki bida zakkar sa amma yayi sallah to sallarsa za’a tsare ta ba zatakai sama ba har sai ya zo da zakkarsa’ idan yazo da ita za’a sanyata ta zama kamar mafi kyawun dawakai suna dauke da sallarsa’ sai su dauketa zuwa kasan Al’arshi sai Allah ta’ala ya ce:” Ka je zuwa Aljanna kai ta gudu a cikinta har zuwa ranar Alkiyama’ duk inda ka kai karshe na gudunka dukkansa damasan da hagunsa ya zama mallakinka’ sai yayi ta gudu gudun da duk taku tazararsa ta kai tsawon tafiyar shekarra guda n zai kyma yi ta a kiftawar idonsa tun daga ranar daya fara har zuwa ranar Alkiyama har sai ya kai ga inda Allah ta’ala ya so ya tsaya’ sai yazmo dukkan wannan tazara waje ta zama mallakinsa da kwatankcinta a damarsa da hagunsa da gabansa da bayansa da samansa da kasansa. Idan kuma yayi rowa bai bayar da zakkarsa ba’ o za’a umarta a dawo masa da sallarsa a likketaa kamar yadda halittu suke likke tufafi jefa masa a fuskarsa’ ace da shi ya kai bawan Allah me zakai d wannan (Sallah) ba tare da wannan ba (Zakka) si ya ce Sai Sahabban Manzon Allh (sawa): Wallahi kai wa yafi munin halin wannan mutumin! Sai Manzon Allah (sawa) ya ce: shin bana gaya maku wanda yafi halinsa yafi wanna muni ba? Sai suka ce: Kwarai kuwa fada mana ya Rasulallah.
Sai Manzon Rahama (sawa) ya ce: -wanda yafi munin yanayi ga wanna mutumin shi ne – Mutumin da ya halarci jihadi a tafarkin Allah aka kashe yana mai tunkarar makiya ba mai juya masu baya ba’ kuma Hurul Aini suna masu dokinsa’ kuma masu kulaa da Aljanna suna shaukinsa suna masu jiran shigowar ruhinsa’ Mala’ikun sama da Mala’ikun kasa suna masu sauraren saukowar Hurul Ein gareshi’ da Mala’iku masu tsaron Aljanna suma suna jiransa zuwan amma sai suga ba wanda zai sakko zuwa gareshi na daga Hurul Eini sai Mala’kun kasa su ce kusa da wannan wanda aka kashen: me yasa Hurull Ein basa sakkowa gareshi kuma me yasa Mala’iku masu tsaron Aljanna basa amsa masa? Sai a kira su daga saman saman 7: Ya ku Mala’iku ku yi duba zuwa sassan bangarorin sama da abunda ke kewaye da ita.
Sai su duba suga cewa: Tauhidin wanna bawa da aka kashe da imaninsa da Manzon (sawa) da sallarsa da zakkarsa da sadakarsa da dukkaan kyawawan ayyukansa gaba daya an dakatar da su a kasan sama kuma sun cika sararin sama gaba daya – kamar wani ayari mai girma da ya cika karshen gabas da yamma da kudu da arewa- mala’iun da ke dauke da wannan ayyuka da sune zasu shiga da su suna cewa: me ke faruwa ba’a bude mana kofofin sama domin mu shiga cikinta da ayyukan wannan shahidin?.
Sai Allah Ta’ala ya bayar da umarnin a bude kofofin sama’ sai bude su bayan an bude sai a kira wadannan mala’iku da ke dauke da ayyukan wannan bawa da su shigo da ayyukan idan zasu iya’ sai ya zamo fuka-fukansu sun gaza dagawa kuma ba zasu iya daga wadannan ayyukan ba sai su ce: ya Ubangijinmu ba zamu iya daga wadannan ayyukan ba. Sai mai kira na ubangiji mai girma da daukaka ya kirasu: ya ku wadanann Mala’iku ba ku ne masu iya daukar wadannan kayan ba sai dai masu daukarsu sune ababen hawa da suke dauke ayyukan ne’ sune zasu dauke su zuwa kasan Al’arshi kuma su ajiye ayyukan akan matakin darajar Aljannah.
Sai Mala’ikun suka ce: ya Ubangijinmu mene ne kuma abinda suke dauke da ayyukansu? Sai Allah madaukakin sarki ya ce: ku me kuka dauko daga gareshi? Sai su ce Tauhidi gareka da Imaninsa da Annabinka. Sai Allah Ta’ala ya ce abunda wadannan ayyuka suke akai sune Wilayar Ali dan uwan Annabina da wilayar A’immah tsarkaka idan kun zo da su tp sune zasu dauke ayyukan kuma su aje su a Aljannah. Sai su duba sai suga shi wanna mutumin ba shi da daya daga cikin wadannan abubuwan da ake bukata’ ma’ana ba ya da wilayar Ali da iyalansa tsarkaka kuma baya da kiyayya ga makiyansu.
Sai Allah tabaraka wata’ala ya ce da wadannan mala’ikun da suke dauke da yyukan bawan: ku kyale su ku koma wajen aikinku na mulkina domin wanda yafi cancanta da ya dauke su ya aje su a agurin daya cancanta. Sai wadannan mala’iku su koma wajen ayyukansu wanda aka sanya su aikin agun.
Sannan sai mai shela na Allah madaukakin sarkin ya ce:ya ku Zabaniyawa ku dauke su ku jefa su a tsakiyar wutar Jahim domin ma’abocinsu bai sanya masu masu daukar su ba na daga wilayar Ali da Iyalansa Tsarkaka As.
Sai Manzon Allah (SAWA) ya ce: sai wadannan Mala’iku Zabaniyawa su dauke ayyukan’ sai Allah ta’ala ya juyar da wadannan ayyukan su koma zunubai da bala’oi akan wanda ya zo da su saboda babu abun hawa na wadannan ayyukan wato wilayar Amiril Muminin Ali As sai wadanann mala’ikun su shelanta sabawar wannan bawa ga Ali As da wilayantar da makiyansa. Sai Allah madaukakin sarki sallada bakaken macizai akan ayyukansa wanda sun zamo kamar hankaku da manyan kwari, sai ya zamo wuta tana rinka faita daga bakunan wadannan Macizai tana mai kona wadannan ayyuka’ bbau wani aikinsa da zai yi saura sai sun lalata shi sai ya zamo wilayarsa ga makiya Ali As da karyatawarsa ga wilayarsa’ wannan shi zai tabbatar da shi a tsakiyar wutar Jahim sai ya zamo aikinsa duga ya lalace kuma zunubansa da laifukansa su yi nauyaya. Wanna shine mafi muni yanayi sama ga wanda ya hana zakka kuma yake kiyaye sallah.
2- Wasu Halaye Na Mu’umini Da Suke Kasancewa Ana Shafe Masa Zunubansa Da Su:
Ya zo a cikin littafin riwayar hadisil Quds ce daga Imam As cewa: “ Ya Musa shin kasancewa wani bawa daga cikin bayani zai aksance yana da zunubai da kura-kurai da suka kai tsororuwar sama amma zan gafarta masa su’ kuma ban damu da yin hakan ba? Sai Annabi Musa As ya ce: “Ya Rabbi ta ya hakan zai kasance amma baka da mu ba? Sai Alla Ta’ala ya ce: “saboda wata kyakkyawr halayya d ta kasance a tare da bawana wacce na ke sonta’ wanna halayyar kuwa ita ce ya kasance yana son muminai talakakawa ‘yan uwansa, yana kulawa da su, kuma yana daidaita kansa da su. Kuma ba ya yin girman kai akansu, idan har ya akaita hakan to zan gafarta masa zunubansa ba tare da na damu ba’’.
3. Illar Yin Alfahari:
Ya zo a cikin littafin riwayar hadisil Quds ce daga Imam As cewa: "Ya Musa As lallai Alfahari mayafina na ne kuma jiji da kai (Taqama) tufafi na ce’ dukkan wanda ya yayi kokarin yin jayayya da ni a wani daga cikinsu zan azabtar da shi da wuta ta”.