8 Mayu 2025 - 14:47
Source: ABNA24
Sheikh Zakzaky (H) Ya Gana Da Iyalan Shahidan Qudus Na 2025

Da yammacin ranar Laraba 9 ga Zulqa’ada 1446 (7/5/2025) Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gana da iyalan Shahidan waki’ar Quds din bana, a munasabar cikansu kwanaki 40 da Shahada, a gidansa da ke Abuja.

A yayin jawabinsa, Jagora Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda tun a bara wani babban hafsan soja ya ba su labarin yunkurin kitsa sharrin da hukumar kasar nan suke yi akan Harka Islamiyyah.

Shaikh (H) yace: “Sun ce, za su san yadda za su yi, su yi wani abu wanda za su ingiza ‘yan uwa. Ma’ana su harzuka su. Kamar yadda suka ce, za su yi wani abu wanda za su tsokani ‘yan uwa. In suka tsokane su, sai su fake da abinda za su yi bayan tsokanan, sai su kai hari gidan Al-Zakzaky”.

Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda suka fara kokarin harzuka ‘yan uwan a yayin jajen Arba’in din Imam Husaini (AS) a watannin baya, inda suka kama ‘yan uwa a hanyar zuwa Abuja ta wajen Suleja, suka kuma afkawa tafiyar Arba’een din da kisa.

Shaikh Zakzaky ya cigaba da bayyana yadda jami’an tsaro suka bi har gidajen mutane a Karmajiji da Suleja, suka kama matan aure da yara, suka kai su hedikwatansu suka cire musu hijabai suka, suka dauki hotunsansu suka yada a intanet. 

Yace, manufar hakan dama kamar neman su tsokano ‘yan uwa ne su harzuka. Saboda sun san “Indai Musulmi ne mai kishin Musulunci, ba abinda ya fi zama cin zarafi a gare shi, kamar a taba mace. Don akan kware Hijabin mace ne aka hukunta Banu Qainuka a Madina”.

Jagora ya yaba da matakin hankalin da ‘yan uwa suka dauka a lokacin, na gudanar da Muzaharori a garuruwa. Yace: “’Yan uwa sun nuna hankali. Aka yi Muzaharori a ko ina, na nuna cewa, ba a yarda da kware ma ‘yan’uwa Hijabi ba”.

Ya bayyana takaicinsa akan yadda masu kafa tebura suna magana da sunan addini, ana sawa a net, ba wanda yace komai akan kware wa mata Musulmi hijabi da jami’an tsaron kasar nan suka yi a lokacin. Yace: “Shiru suka yi da bakinsu suka yi gum.” Ya kara da cewa: “Mun san kuma wallahi in da mu ne, aka taba wata mace, ko meye aqidarta, - kamar yadda suke cewa. Ko kuma ra’ayinta. Ba za mu yarda da wannan ba”.

Shaikh Zakzaky ya bayyana aikin jami’an tsaron a matsayin tsararren tsokanan da ya kwaranye ba tare da cimma nufinsa ba. Yace: “Wannan tsokana da suka yi, ya isa su fake da wannan su kai hari gidan Al-Zakzaky kamar yadda suke bukata. To amma sai suka farga da wani abu da basu sani ba. Shi Al-Zakzakyn baya nan, ya tafi Iraq, yana can Karbala. 

“Sai suka ce, ah! Ai ba za su iya fakewa da wannan su je gidansa ba, tunda bashi nan ma. To sai ya zama shikenan, ba su iya zuwa gidan nasa ba ma. Sun dai yi hayaniyarsu. Amma sun kama ‘yan uwa, har yanzu zancen da muke yi akwai ‘yan uwa 33 a tsare a kurkukun Keffi akan wannan, wai ana tuhumarsu da wai sun kashe ‘yan sanda”.

Shaikh Zakzaky ya bayyana waki’ar Quds ta bana a Abuja a matsayin sabon shirin hukumar kasar nan na yunkurin cimma mugun nufinsu akan Harka. Yace, dama tun farko sun ma Quds shiri, suka ba da sanarwar cewa, za a yi Quds na duniya a duk fadin duniya, kuma a nan Nijeriya ana sa ran za a yi a garuruwa kaza da kaza, amma ba za a aminta da Islamic Movement wanda Al-Zakzaky ke jagoranta ba, saboda an sansu da ta da tarzoma, saboda haka ana tsammani za su ta da tarzoma ne”.

A nan ne Shaikh Zakzaky ya mai da amsa da cewa: “Nasan wanda duk yake rubuta wannan, ya tabbatar karya yake yi! Domin duk wani wanda yake da unifom yanzu, tun daga ‘Chief of Defense Staff’, har zuwa kurtu da ake dauka yanzu; da kuma tun daga ‘I.G’ na yanzu, har zuwa kurtu, gabadayansu tun kafin su sa kaki muke wannan aikin (na Da’awar Harkar Musulunci)”.

Yace: “Ka san duka-duka mutum zai shekara da kaki 35 ne ko? To mu yau shekara 48 muna abinmu. Yaushe za ka zo kace mana rana daya wai mu wani abu ne daban? Tun kana firamare ko sakandire muke aikinmu. Da yawansu sun bude ido sun ganmu muna abubuwan da muke yi ne. Irin wadanda ake tura su suke harbe-harben nan kuma duk galibansu kafin a haife su ne muke harkokin. Wani hatta uwarsa ma ba a aure ta ba! Yanzu yana da unifom yana harbi, amma lokacin da muka fara harkokin nan uwarsa ma ba a aure ta ba ma tukunna. Tunda ga yaranmu nan ma sun giggirma. Amma wai mu ne aka sani da ta da tarzoma, saboda haka ba a aminta cewa za a yi a gama lafiya ba?”.

Jagora ya bayyana yadda aka yi Muzaharar ta Quds din bana a birane 35 a Nijeriya, ko ina aka tashi lafiya, in banda Abuja da sojojin da suke gadin shugaban kasa suka bayyana suka bude wuta da bindiga. 

Ya kuma bayyana irin ta’addancin da sojojin suka yi, wanda ya hada da, haduwar soja bakwai akan wata mace daya suna cin mata mutunci, da kokarin kware mata hijabi. Da kuma harbe-harbe da kwashe mutane su tursasasu a barikokin soja daban-daban, kafin daga baya su kai su wajen ‘yan sanda, da kin kai su asibiti alhali suna cikin munanan raunuka, da sauransu.

Shaikh Zakzaky ya bayyana al’ajabinsa akan irin wannan ta’addanci na gwamnatin Nijeriya. “Abinda yake daure min kai, wai to meye ma’anar harbi ne a nan?” Ya kara da cewa: “Mu kaddara ba ku son wannan muzaharar ta ranar Quds, da ma ba muna tsammanin za ku so ba ne. To amma idan ba ka son abu, sai wani ya yi, to sai ka kashe shi? Mun ji kai kake da gwamnati. To in kai kake da gwamnati in wani ya yi abinda ba ka so, to kashe shi za ka yi?

“Hatta ko da doka ce tace, duk wanda yake da gwamnati, ko kuma gwamna, in wani ya yi abinda baya so, ko kuma baya son mutumin, to yana iya kashe shi. Ko da doka ce tace haka nan, to dole dokan ta yi tanajin yadda za a yi kisan ko? Ba za ta ce kawai soja su je su samu mutumin su bude mashi wuta ba ko? Kila za ta ce ne a kama mutum, a kai shi kotu, ace gashi ana tuhumarshi da laifi, wanda irin wannan laifin duk wanda ya aikata shi kashe shi ake yi. To sannan kotu ta ga ganinta, taga ko ya cancanci a a kashe shi, sannan ta yanke hukunci na kisa. Sannan a bi matakai a kashe. Amma wannan kun je ne kawai kuna dambara harsashi akan mutane”.

Jagora yace: “Wannan karon da suka samu abinda suke so, suka bude wuta, yanzu ya ishe su suce sun samu dalili sun tsokani mutane, sai kuma su je gidan Al-Zakzaky ko? Tunda dama abinda suke so su yi kenan”.

Yace: “Aikuwa (tunda) haka suka zata. Sai suka ce wai, an harbi soja guda daya da bindiga. Saboda haka, Shi’a suna da bindiga.” Yace: “Bindiga fa guda daya kenan aka harbi mutum daya, amma kuma (suka ce) duk Shi’a suna da bindiga. Saboda haka, za a bi duk inda (Shi’an) suke, unguwannin da suke a yi abinda suka kira ‘binciken da za a rutsa da wurin.” Wato za a rutsa da unguwar ne ya zama ba shiga ba fita, soja kawai zai rutsa da adadi mai yawa. Soja mota 120, sun ce za su kewaye unguwa, su shiga gida-gida, wai suna binciken bingidar da aka harbi soja guda daya. Kuma za su yi wannan a duk unguwannin da ‘yan uwa suke ne”.

Yace: “Inda suka tona ma kansu asiri, shi ne da suka ce, in sun kashe mutum za su tafi da gawarsa. To kun ga sun ce me za su je su yi kenan? Za su je su yi kisan kai ne a gida-gida. To kuma cikin wuraren da za su je su yi binciken har da gidana”.

Shaikh Zakzaky ya tambaye su da cewa: “Mu kaddara wani ‘Shiite’ – kamar yadda suke cewa, ya yi harbi, in Shiite din ya yi harbi din, me zai sa ya kai bindigar gidan Al-Zakzaky?”

Yace: “In dagaske ne ya yi harbin (ma kenan). Ballantana sun sani sarai cewa, in ma da gaske ne an yi harbin, to wani soja ne ya harbe shi, tunda su suke da bindiga, kuma su suke harbi.” Ya kara da cewa: “Sanannen abu ne, in (soja ko dansanda) suna ‘operation’, suna samun harbe-harbe tsakaninsu, ko da gangan, ko da kuskure. To amma da yake ko babu wani dalili, in suka yi abu, to mu ne muka yi laifi. Ko (su ce) mun tsare musu hanya, ko wani abu. Duk abinda ya faru mu muka ja, ko da dayansu ya kashe kansa. Ballantana wannan mun san shiri ne”.

Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda sojojin bayan da suka ga labarin shirinsu ya bazu, sai suka dawo suka ce sun gano cewa wani soja ne ya harbi dan uwansa sojan. Yace: “To sai daga baya suka ce, wai shi wannan sojan, wani soja ne ya harbe shi.” Yace: “Amma lokacin da labari ya bayyana cewa sun shirya za su je gida-gida su yi bincike, basu musanta ba. Sai suka yi shiru da bakinsu. Ka san da ba da gaske ba ne, nan da nan za su musanta, amma sai suka yi gum da bakinsu”.

Yace: “Wato kenan, ta kowane hali suna neman wani sanadi da za su fake, su je inda muke kwana su kashe mutane. Kawai dama aniyar kenan”.

Da yake bayani dangane da yadda Yammacin duniya, irin su Amurka da Birtaniya ke tsoma baki akan al’amarin Quds a kasar nan, Jagora ya bayyana cewa: “Sun dauki su mahukuntan kasar nan da jami’an tsaronsu tamkar karnuka ne, ba bil’adama ba. Basu dauke su a bil’adama ba, domin su a can ana yin (Muzaharar Quds) ba su yin komai, amma suna ce ma na nan ku kashe. Suna umurtansu su yi kisa, kuma suna yi”.

Yace: “Na ji ma aka ce, takardar da aka ce mai ba shugaban kasa kan sha’anin tsaro, da aka ce ya rubuta. Sai wani jami’in tsaro yake gaya mana cewa, ba dole ne ya zama shi ya rubuta ba. Akwai wata Ba’amerikiya, tana aiki a wurin (ofishinsa), ita ta rubuta. Kuma bai isa ya ce ba shi ne ba”.

Shaikh Zakzaky yace: “Tir! Ka zama kare! Baka da mutunci. Ka rike mukami, Ba’amerike ya rubuta abu da sunanka amma ka yi shiru. Wannan zilla (kaskanci) har ina?”

Ya ja hankalin mahukuntan Nijeriya akan su zama mutane. “Abin da daure kai! Har yaushe ne za ku yi dabi’a irin na bil’adama? Ku zama mutane mana. In ma baku da addini, to ku zama ‘yantattu mana? Don me kai za ka zama wani ne zai zo yace maka ka kashe mutum, kai kuma sai ka kashe?”

Ya jaddada musu cewa akwai sakamako akan abin da suke yi. “To in ma ku ka dauka, kun kashe mutum ba abinda zai faru. Haka kuke gani. To ba gaskiya ba ne! Ba yadda za a yi ka kashe mutum, shikenan zance ya kare. Akwai hukunci a nan duniya… Ba za ka gama lafiya ba, ba kuma za ka ga da kyau ba! Ba wanda ya taba kisan kai ya kare lafiya. In baka yarda da lahira ba kenan. Baka yarda da cewa in an mutu ana tashi ba. To kuma in an mutu ana tashi, akwai hukuncin Lahira na tafe. 

“In kai Musulmi ne, to za ka gamu da jaza’in da ke cikin fadin Allah Ta’ala: “Wanda ya kashe mumini da gangan, sakamakonsa jahannama ne…” Saboda haka kar ka kashe mumini”.

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi albishir da rashin dauwamar zalunci. “Da yake mu an far mu da kisa, amma mun san ba iyakanta kenan ba. Dama wannan rayuwar ba iyakanta kenan ba, akwai sakamako na kusa akwai na nesa. Jinanen da aka shekar ba za su tafi kawai ba. Akwai sakamako na kusa, akwai sakamako na nesa”.

Ya jaddada jaje ga iyalan wadanda aka kashe musu ‘yan uwa, mazaje, mataye, iyaye, ‘ya’yaye, makusanta da masoyansu. Tare da musu nasihar dauriya da addu’ar samun lada. “A daure, a daure, Allah Ya kambama ladan dauriya”.

A karshe, Jagora ya yi addu’ar Allah Ya karbi wadanda aka kashe a matsayin Shahidan da yake azurtawa. Ya kuma yi mana sakayya, akan mahukuntan kasar nan, - ma’aikatan Turawan Yammacin duniya. “Allah Ta’ala ya tozarta su, tun a nan duniya, kafin tozartan lahira, Ya kawo mana mummunan karshensu. Allah muna rokonka ka bi hakkin jinanen wadannan da aka shekar, akan wadanda suka yi harbi da hannuwansu, wadanda suka yi kisan, da kuma wadanda suka saka su, da wadanda suka yi umurni daga waje, su ma Allah ka kawo mana mummunan karshensu duk cikansu”.

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

09/Zulqada/1446

07/05/2025

Your Comment

You are replying to: .
captcha