9 Mayu 2025 - 14:36
Source: ABNA24
Jagora: Dangane Da Ilimin Fikihu, Wadannan Abubuwan Suna Da Kyau A Yi La'akari Da Su

Na farko, fikihu amsoshin addini ne ga bukatu a aikace na dai-dai kun mutane da al'umma. Tare da haɓakar kaifin hankali na canjawar tsatso, wannan bukatun dole ne, a yau fiye da kowane lokaci, su kasance suna da tushe mai tushe na hankali da na ilimi, kuma su zamo wadaanda za’a iya fahimta da ganewa.

Maudu'i Na Farko Shine Taken "Hauzar Ilimi" Da Zurfin Abunda Ke Cikinta.

Adabi da yake yaduwa dangane da wannan batu gajere ne kuma bai wadatar ba. Sabanin abin da wannan Adabi ya ke nunawa, fagen ba wai kawai cibiyar koyarwa da koyo ba ne, a'a, kunshi ne na ilimin kimiyya, tarbiya, da ayyukan zamantakewa da siyasa. Za a iya zayyana ma'aunai daban-daban na wannan ma'anar kalmar kamar haka:

1- Cibiyar kimiyya tare da kebantattun ƙwarewa;

2- Cibiyar horar da malamai masu wayewa da nagarta don jagoranci addini da dabi’u na al’umma;

3- Jagoran gaba wajen tunkarar barazanar makiya a fagage daban-daban;

4- Cibiyar samarwa da bayyana tunanin Musulunci kan tsarin zamantakewa; Tun daga tsarin siyasa da siffarsa da abin da ya kunsa, da tsare-tsaren da suka shafi gudanar da kasa, da tsarin iyali da alakar mutumtaka, bisa tsarin fikihu da falsafa da tsari mai kima na Musulunci;

5- Cibiyar ko kuma za’a iya cewa tsororu sabbin kere-kere na wayewa da hangen nesa da ya wajaba a samar da su a cikin tsarin sakon Musulunci na duniya.

Waɗannan kanun batutuwa su ne suka ayyana kalmar "Hauza Ilmiyyah" da kuma nuna abubuwan da ke tattare da ita, da ke da ma'anar, "tsammanin" abunda za’a samu a cikinta. Kuma waɗannan ne zaburantarwaa da ƙarfafawa wajen ci gaba da bunkasarta kuma zai iya sanya Hauza ta zama " mai ci gaba da yin  fice" a haƙiƙanin ma'ana da magance kalubale da barazanar da ke gaba.

Akwai hujjoji da ra'ayoyi game da kowane ɗayan waɗannan batutuwa, waɗanda za a iya taƙaita su kamar haka:

Farko - Cibiyar Kimiyya:

Makarantar hauza ta Qum ita ce ta gaji babban jarin kimiyyar Shi'a. Wannan tarin na musamman ya samo asali ne daga tunani da bincike na dubban malaman addini a ilimomi kamar fikihu da tauhidi da falsafa da tafsiri da hadisi a cikin tsawon shekaru dubu.

Kafin binciken kimiyyar dabi'a a karnin baya-bayan nan, an dauki fannonin kimiyyar Shi'a a matsayin fagen mu'amala da sauran ilimomi. Amma a kowane lokaci, babban abin da aka fi mayar da hankali kan tattaunawa da bincike a Hauzozi shi ne "ilimin fikihu" sannan kuma tare da wata yar tazara aka samar da "Tauhidi, Falsafa, da Hadisi."

Ci gaban fikihu sannu a hankali a cikin wannan dogon zamani tun daga zamanin Sheikh Tusi zuwa zamanin Muhaqqiq Hilli, daga nan kuma har zuwa Shahid, daga nan kuma har zuwa Muhaqqiq Ardebili, daga nan kuma har zuwa Sheikh Ansari, har zuwa wannan zamani, abu ne da malamai ke iya gani irin ci gaban. Ma'auni na ci gaban ilimin fikihu shine ƙarawa ga ilimin da ake da shi, wato, samar da ingantattun samfuran kimiyya da haɓaka matakin ilimi da sabon binciken. Amma a yau, idan aka yi la'akari da saurin canje-canje masu sauri na tunani da ilimi a wannan zamani, musamman a cikin karnin da ya gabata, dole ne a yi la'akari da ƙarin tsammanin samuwar wasu ci gaba a fagen ci gaban ilimin Hauza.

Dangane Da Ilimin Fikihu, Wadannan Abubuwan Suna Da Kyau A Yi La'akari Da Su:

Na farko, fikihu amsoshin addini ne ga bukatu a aikace na dai-dai kun mutane da al'umma. Tare da haɓakar kaifin hankali na canjawar tsatso, wannan bukatun dole ne, a yau fiye da kowane lokaci, su kasance suna da tushe mai tushe na hankali da na ilimi, kuma su zamo wadaanda za’a iya fahimta da ganewa.

Bugu da ƙari, bayyanar sabbin abubuwa masu yawa wuyar sha’ani a cikin rayuwar mutane a yau suna haifar da tambayoyin da ba a taɓa yin irin su ba waɗanda fikihu na wannan zamani dole ne su sami cikakkun amsoshinsu.

Bayan haka, a yau ta hanyar kafa tsarin siyasar Musulunci an samu, babban abin tambaya shi ne, ta yaya shari’a take kallon fagagen daidaiku da zamantakewa na rayuwar dan Adam da asasinsa. Tun daga dubi na daidaikun mutum da matsayinsa na mutuntaka da manufofin rayuwarsa, zuwa kallon yanayin zamantakewar bil'adama, da kallon siyasa, mulki, zamantakewa, dangi, nau’in halitta namiji da mace, adalci, da sauran bangarorin rayuwa. Fatawar malaman fikihu a kan kowace mas’ala ya kamata ta yi nuni da wani bangare na wannan mahanga mai fadi.

Muhimmin abin da ake bukata wajen cimma wadannan siffofi shi ne, na farko malamin fikihu ya san dukkan bangarori da ilimin addini a dukkan fage, na biyu kuma ya dace da sanin sabbin abubuwan da aka gano a yau a fagen ilimin dan Adam da ilimin da ya shafi rayuwar dan Adam.

Dole ne a yarda cewa tarin ilimin da aka tara a cikin wannan fanni yana da damar da zai iya kai dalibi zuwa wannan matakin na ilimin kimiyya, idan kuma an ga wasu abubuwan da ke cikin hanyar aikinsa a magance su tare da budadden idon basira kuma a gyara su da hannu.

Ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan shine tsawon lokacin karatun. Lokacin karatun ɗalibin ana gudanar da shi ne ta hanyar da ta dace; An tilasta wa ɗalibin yin nazarin littafi mai zurfi, na wani babban malami ya yi bincike a matsayin littafin karatunsa. Wannan littafi a haƙiƙa yana da alaƙa da lokacin da ya shiga fagen bincike na ijtihadi ne, kuma ana ba shi littafin tun kafin wannan matakin ba zai ƙara tsawaita lokacin karanta nassin ba. Littafin ya kamata ya ƙunshi batu da yaren da ya dace ga ɗalibin na ɗan lokaci kaɗan kafin shiga lokacin bincike. Kokarin nasara ko rashin nasara da manyan mutane irin su Akhund Khorasani, Hajj Sheikh Abdulkarim Haeri, da Hajj Sayyid Sadruddin Sadr suka yi na maye gurbin litattafai irin su Qaani, Rasa’il, da Fusul da Kifayah, Durr al-Fua’id, da Khulasat al-Fusul, an yi su ne da wannan muhimmiyar larura ne. Ko da yake sun rayu a lokacin da ɗalibai ba su fuskanci ɗimbin abubuwan da suka shafi tunani da kuma ayyuka masu amfani da suke fuskantarmu a yau ba.

Wani batu kuma shi ne batun fifikon fikihu. A yau, da samar da tsarin Musulunci da gabatar da tsarin tafiyar da salon Musulunci, al'amura masu muhimmanci sun zama masu fifiko a fagen da ba a yi la'akari da su a baya ba a Hauza. Batutuwa kamar alakar hukuma da al'ummarta da sauran jihohi da al'ummomi, da batun kawar da tafarki, tsarin tattalin arziki da asasinsa, tushen tsarin Musulunci, tushen mulki daga mahangar Musulunci, matsayin al'umma a cikinta da daukar matsaya kan muhimman batutuwa da adawa da tsarin mulkin mallaka, tunani da abin da ya kunsa na adalci, da kuma wasu muhimman al'amurra na yau da kullum, da sauran muhimman al'amurran da suka shafi kasar nan gaba, da sauran muhimman batutuwan da za su kasance a gaba, da sauran muhimman batutuwan da suka shafi yau da gobe dukansu suna bukatar amsa fikihu. (Wasu daga cikinsu kuma suna da bangaren tauhidi da ya kamata a yi magana a kansu).

A halin yanzu yadda ake yin aiki a makarantar hauza, a cikin sashin shari'a, ba a ba da isasshen kulawa ga waɗannan abubuwan da suka fi dacewa ba. Wani lokaci muna ganin cewa wasu fasahohin kimiyya, wadanda gaba daya suna da wani bangare na dabi'a kuma su ne na share fage wajen kaiwa ga hukuncin shari'a, ko wasu lamurra na fikihu ko na asasi a wajen abubuwan da suka fi dacewa da su, don haka suna nutsar da fikihu da mai bincike a cikin su da batutuwa na zakinsu da dacinsu ta yadda sukan shagaltu da tunaninsa gaba daya daga wadannan manyan batutuwa da fifiko da sadaukar da damammaki da ba za a iya maye gurbinsu ba da dan Adam da dukiyar kudi ba, ba tare da bayar da gudummawa da fayyace yanayin rayuwar al'ummar Musulunci ba wajen tunkarar kafirci.

Idan hadafin aikin kimiyya ya zamo shi ne nuna fifikon kimiyya da suna da gasa wajen bayyanar da nagarta, zai zama misali na aikin jari-hujja da abin duniya kamar yadda wannna ayar take fada “Kuma ya dauka Ubangijinsa ya zama shineson ransa”.

Your Comment

You are replying to: .
captcha