4 Satumba 2024 - 18:59
Manzon Rahama (SAWA): Idan Kuka Sanyawa Yaro Suna Muhammad To Ku Girmama Shi Kuma Ku Buda Masa A Wajen Zama Kuma Kada Ku Munana Masa Fuska.

Bisa tunawa da zagayowar ranaar shahdar Imam Aliyu dan Musar Ridah As ABNA ta kawo maku wasu daga cikin gwalagwalan hadisai daga cikin littafin sahifatur Rida As:

Bisa tunawa da zagayowar ranaar shahdar Imam Aliyu dan Musar Ridah As ABNA ta kawo maku wasu daga cikin gwalagwalan hadisai daga cikin littafin sahifatur Rida As:

1- Da Isnadinsa daya tuke ga Annabi sawa daga Allah ta’ala yana cewa: La ilaha Illal lahu mafaka ta ce duk wanda ya shiga mafaka ta ya ya samu amina daga azaba ta.

2- Da Isnadinsa daga Annabi sawa ya ce: mutne uku zan cece su ranar alkiyama’ wanda ya girmama zuriyata’ da wanda ya biya masu bukatarsu’ da wanda yake dawainiya da su a lamuransu idan sun bukata gareshi’ da mai son su da zuciyarsa da harshensa.

3- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa ya ce: Imani tabbatarwa ne da harshe da sani a zuciya da kuma aikin da gabbai.

4- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa daga Allah ta’ala yana cewa: ya kai Dan Adam ba zakmain adalci ba ina sonka da ni’imomina’ kai kuma kana sakamin da sabonka’ alherina gareka mai sankowa ne’ amma shirkarka tana zuwa gareni’ kuma mala’ika mai karamci ba ya gushewa yana zomin daga gareka ako wace rana da dare da mummunan aiki’ ya kai daan Adam da ace zakaji siffar yadda kake daga waninka kuma kai bakasan wanda ya siffanta ka ban da ka yi gaggawar wajen kiyayyarsa.

5- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa daga Allah ta’ala yana cewa: Babu wani abun halitta da zai nemi mafaka koma bayana ga wani halittar sai na yanke hanyoyin albarkar sammai da kassai daga gareshi’ idan ya rokeni ba zan amsa masa ba’ idan ya kirani ba zan amsa masa ba’ kuma babu daga cikin abun halitta da zai nemi mafaka gareni koma bayan halittuna sai na tanadar masa da arzikinsa sammai da kassai.

6- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa yana cewa: ku yi wa yaranku kaciya a rana ta bakwai da haihuwa domin shine maafi tsarki kuma masu saurin cirar nama.

7- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa yana cewa: Ilimi taskoki ne da shi kuma mabudanta tambaya don haka ku rinka tambaya domin a cikin tambayar ana bawa mutum hudu lada’ mai tambayar da malamin da wanda ya ji da wanda yaso hakan.

8- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa daga Allah ta’ala yana cewa: Ya kai dan Adam kada zunubin mutane ya rudeka daga barin naka zunubin’ ko wata nu’ima ta rude ka daga barin taka ni’imar’ kar yanke mmutnae daga samun rahamar Allah Ta’ala alhali kai kana fatan samunta ga kanka.

9- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa yana cewa: Abubuwa guda uku ina jiyewa Alumma tsoronsu a bayana’ bata bayan sani’ da fitinoni masu batarwa’ da sha’awar ciki da faraji.

10- Da Isnadinsa daga Manzon Rahama sawa yana cewa: Idan Kuka Sanyawa Yaro Suna Muhammad To Ku Girmama Shi Kuma Ku Buda Masa A Wajen Zama Kuma Kada Ku Munana Masa Fuska.