A cikin yanayin ruhiyya da rayuwar ibadar Imam Riza (a.s) an bayyana cewa yana da karancin barci kuma yana yawan azumi, kuma bai taba barin yin azumin kwana uku a kowane wata ba, kuma yana cewa: “Duk wanda ya yi azumin kwana uku na kowane wata to kamar ya azumci dukkan rayuwarsa gaba daya ne”. (1).
Yayin da ya bayar da rigarsa kyauta ga Da’abal, ya ce da shi: “Da’abal, ka kasan girman wannan rigar ka kiyaye ta da kyau! Domin na yi salla da ita darare dubu ako wane dare raka'a dubu kuma na sauke Qur'ani sau dubu a wadannan darare.
1). Uyuni Akhbar Reza (AS), juzu'i na 2, shafi na 184.
2). Bihar al-Anwar, juzu'i na 79, shafi na 309.