2 Satumba 2024 - 11:27
Bayyanar Adalci Cikin Rayuwar Zamantakewa A Cikin Gwamnatin Annabi Muhammad (SAWA)

A zamanin hukumar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa’Alihi Wasallama, adalci acikin zamantakewa ba wai kawai wani hadafi ne mai muhimmanci kadai ba, a’a har ma shi ne babban ginshikin tsarin zamantakewa da siyasa na al'ummar musulmi. Manzon Allah (SAW) ya kafa al’umma bisa adalci da daidaiton hakki ga kowa da kowa ta hanyar jaddada adalci da daidaito.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (AS) / ABNA:

Daya daga cikin muhimman siffofi na gwamnatin da Manzon Allah (saww) ya kafa wanda ke bambanta ta da sauran gwamnatoci shi ne tabbatar da adalci a cikin al'umma a kowane bangare na rayuwar mutane. A cikin wannan gwamnati, an aiwatar da adalci ba kawai a cikin dangantakar daidaiku ba har ma a matakin al'umma da cibiyoyin gwamnati. Alkur’ani mai girma da Sunnar Manzon Allah (SAW) cike suke da umarni da nasihohi da suke gabatar da adalci a zamantakewa a matsayin wani aiki na addini da na dabi’a.

1. Adalci wajen rabon dukiya

Daya daga cikin fitattun abubuwan da suka bayyana na adalci na zamantakewa a cikin gwamnatin annabta shi ne adalcin raba dukiya da albarkatu tsakanin mutane. Manzon Allah (S.A.W) ya jaddada hakkin wanda ake zalunta da mabukata, ya kuma dauki wannan a matsayin daya daga cikin manyan ayyuka na gwamnatin Musulunci. Ya zo a cikin Alkur'ani mai girma cewa: "don ka da dukiya ta zamo kawai ta takaita tsakanin masu kudinku" (Suratu Hashr, aya ta 7).

«کَیْ لَا یَكُونَ دُولَةً بَیْنَ الْأَغْنِیَاءِ مِنْكُمْ»؛

Don haka anayin adalci wajen rabon dukiyadon ka da ta zamo kawai masu kudin cikiunku suna hannu da hannu da ita komawa bayan sauran al’umma. Wannan ayar ta yi bayani karara kan muhimmancin rabon dukiya a cikin al’ummar Musulunci.

Haka nan Manzon Allah (SAW) ya ba da kulawa ta musamman ga zakka a matsayin daya daga cikin manyan hanyoyin raba dukiya. Zakka ba ibada ce kadai ba, har ma ta kasance hanyar tabbatar da adalci a cikin al’umma, wacce aka ware ta kai tsaye ga mabukata da miskinai (1).

2. Adalci wajen yin hukunci da warware sabani a cikin gwamnatin annabci.

Yin hukunci ya ginu ne bisa ka’idojin adalci da gaskiya. Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana daukar adalci a matsayin babban ma'auni wajen warware sabani da yin hukunci tsakanin mutane. A cikin wani hadisin Annabi (SAW) ya ce: « إذا حكمتم فاعدلوا؛» “Idan za ku yi hukunci, ku yi hukunci da adalci.” (2) Wannan umarni mai sauƙi amma mai zurfi ya nuna himmar gwamnatin Manzon Allah a kan adalci a kowane mataki.

3. Adalci akan hakkin tsiraru da raunana.

Manzon Allah (S.A.W) ya jaddada kare hakkin tsiraru da raunana kuma bai taba bari a yi watsi da hakkin wadannan gungu a cikin al'umma ba. Daya daga cikin misalan wannan lamari a sarari shi ne Mu’amalar Manzon Allah (SAW) da Yahudawan Madina wadanda duk da bambancin addini, suna da cikakken ‘yancin zama dan kasa. A yerjejeniyar Madina, wadda take daya daga cikin muhimman takardu na gwamnati a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam, an amince da hakkokin dukkanin bangarori na al'umma da suka hada da tsirarun addinai.

Alkur'ani mai girma ya kuma jaddada adalci wajen mu'amala da wadanda ba musulmi ba:

«لَا یَنْهَاكُمُ اللَّهُ عَنِ الَّذِینَ لَمْ یُقَاتِلُوكُمْ فِی الدِّینِ وَلَمْ یُخْرِجُوكُمْ مِنْ دِیَارِكُمْ أَنْ تَبَرُّوهُمْ وَتُقْسِطُوا إِلَیْهِمْ إِنَّ اللَّهَ یُحِبُّ الْمُقْسِطِینَ»؛

"Allah ba ya hana ku kyautatawa da yin adalci ga wadanda ba su yake ku a cikin addininku ba, kuma ba su fitar da ku daga gidajenku ba, Allah yana son masu adalci." (Suratul Mumtahnah, aya ta 8)(3). Kun ga kenan Allah yana umartarku da ku kyautatawa tare da yin adalci ga waxanda ba su yaqe ku a cikin addini ba, kuma ba su fitar da ku daga qasashenku ba.

Adalci na zamantakewa a zamanin Manzon Allah (saww) a matsayinsa na daya daga cikin asasi na tushe ya taka muhimmiyar rawa a tsarin zamantakewa da siyasa na al'ummar musulmi. Ta hanyar jaddada adalci da daidaito da kuma mutunta hakkin kowa, Manzon Allah (SAW) ya samar da wata al’umma wadda dukkanin mutane ba tare da la’akari da kabilarsu ko addininsu ko matsayinsu ba, suna da hakki daidai da adalci. Wadannan ka'idoji da dabi'u na iya zama ingantaccen abin koyi ga al'ummomin yau.

________________________________________________

 

Madogara:

Alqur'ani mai girma, Surah Hashr, aya ta 7.

Sahihul Bukhari, Kitab al-Ahkam, hadisi na 7050.

Alqur'ani mai girma, suratu Mutahnah, aya ta 8.