A irin rana 23 ga watan safar ne shekara ta 11 bayan hijira ne rashin Lafiyar Manzon Rahama
SAWA ta tsananta wanda takai har Bilal Ya kira Sallah Amma Manzon Rahama SAWA
saboda tsananin rashin lafiya bai ji ba, nan da nan Ummmul Mu’umina Aisha tace
ku cewa Baba na Abubakar ya je yaja Sallah, Ita Ummul Mu’umina Hafsah tace ku
cewa Babana Umar ya Ja sallah.
Manzon Rahama SAWA yana jin wannan zancen nasu duk da cewa yanayin jikin sa ya tsananta amma ya tashi yana mai dora hannayen sa kan kafadun Imam Ali AS da Fadl dan Abbas Rh ahankali suka kaiga masallaci yana mai jan kafarsa ahankali suna isa sai yaga Abubakar yana tsaye a Mihrabinsa wajen Sallar sa yana mai jan sallah.
Manzon Rahma SAWA sai yayi nuni da hannayen sa masu Albarka kan Abubakar ya ja da baya sanna shi kuma ya shiga Miharabin sa wajen sallar ya jagoranci Sallar bayan ya gama sallah ya koma gida cikin tsananin rashin lafiya.
Ganin haka Musulmai sukai ta kuka sosai....
Sannan a ranar 25/Safar/11h A irin wannan rana Raziyyatu Yaumul Khamis ta faru wanda Manzon Rahama SAWA ya bude idunuwan sa masu Albarka ga sahabbansa a zaune a kewaye da shi yace dasu: Ku kawo min abun rubutu da tawada domin na rubuta maku abu saboda karku bata a bayana wasu daga cikin Mutanan dake wajen suk ace a kawo takaradar wani kuma yace kar a kawo tare da fadin wata mummunar Magana wadda a karshe yace littafin Allah ya Ishe su.
Wannan abun da ya faru shi ake kira da Raziyyatu Yaumul Khamis. Wato wata masifa da jarabawa da Allah Ta’ala yayi wa Sahabban Annabi Gaba daya wasu sun samu cinye wannan jarabawa wasu kuma sun fadi. Allah Ta’ala ya tabbatar da mu kan bin Umarnin Annabi SAWA.
Bayan hakan sahabbai sun ta tattauna maganar a gaban Annabin Rahama SAWA har takai yace su tashi su bashi wuri bai kamata suyi jayayya da daga murya agaban sa ba anan kuwa suka fita.
Wanda Imam Ali bayan wannan abu ya faru sauran sahabbai sun fita ya rage sauran kadan daga cikin su wanda suka hada da Salmanul Farisi Da Abu Zarril Gifary Da Miqdad Rh Manzon Allah SAWA ya umarci Imam Ali As daya kawo abun rubutun inda ya kawo, sannan Annabi ya fadi abunda yake son a rubuta wanda Mala’ika jabrail ya sanar dashi domin yasan hakikani tabbas wannan Al’umma nan bada dadewa ba zasu shiga cikin sabani da junan su da shiga bata bayan baya nan wanda su wadanan sahabbai din suka sheda kan abunda Annabi SAWA ya fada Imam Ali AS kuma ya rubuta shi.
Kuma acikin wannan takaradar da ya fada aka rubuta ya anbaci sunayen A’imma da sune wajibi ga Al’ummar sa su bisu na farkon su Imam Ali Da Imam Hasan da Imam Husain As da kuma Imamai tara daga yayan Imam Husain As.
Wandan wasu da dama sun anbaci wanda ya hana kawo abun rubutun a ruwayoyin su wasu kuma sun kawo ruwayar ba tare da anbaton wanda ya fade ta ba
Ala kulli halin dai ya kamata Al’umma su gane cewa Manzon Allah SAWA ya bar masu wasiya kuma tananan karara kamar hasken Rana ya rage nasu da su komawa wannan wasiya daya bari tun kafin lokaci ya kure masu
26/Safar/11h A irin wannan rana ne a shekara ta 11 bayan hijira, Annabi (SAW) ya umarci sahabbai da dama, musamman Manyan Sahabbai su Abubakar da Umar da Usman, da su shirya tafiya zuwa Rum don yakar Rumawa bisa jagorancin Sahabin Nan Usama Dan Zayd, amma suka ƙi bin wannan umarni. Domin suna kin jagorancin Usama ga rundunar manzon Allah SAWA Sai Annabi Sawa ya ce: “Ya Allah ya la’anci duk wanda ya sabe daga rundunar Usama.”duk da haka Abubakar, Umar, da Usman sun karya doka sun dawo sunki bin wannan Runduna.
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana ɗaukar Romawa a matsayin babban haɗari. Don haka ne, a shekara ta takwas na hijra, ya aika runduna karkashin jagorancin Ja’afar bn Abi Talib, Zayd bn Haritha, da Abdullah bn Rawaha zuwa yakin Mu’utah; Amma duk kwamandojin Annabi guda uku da suka halarci yakin sun yi shahada.
A shekara ta tara bayan Hijira, lokacin da Manzon Allah ya ji labarin mamayar da Rumawa suka kai wa kasashen Musulmi, shi da kansa ya tafi yakin Tabuk tare da mutane dubu talatin, amma ya koma Madina ba tare da sun yi arangama da su ba.
A cikin kwanaki na ƙarshe na rayuwarsa, a cikin wannan mawuyacin yanayi lokacin da babban birnin musulunci na Madina ke cike da wannan yanayin na bakin ciki, Manzon Allah (SAW) ya ɗauki wani muhimmin mataki wanda ya cancanci a yi la’akari da shi sosai. Ya yi kira ga rundunar Musulunci ta sahabbai da su yaƙi Daular Rum karo Biyu. Wanda zuwa wannan yakin ya na da nisa, ya ɗaga tutar jihadi da hannunsa mai tsarki ya miƙa shi ga "Usama", wanda matashi ne sosai a wannan rana, ya naɗa shi kwamandan wannan Rundunar, wanda shugabannin muhajirai da Ansar. Abubakar Umar da Abu Ubaydah dan Jarrah, suna karkashin wannan runduna, haka ya umarce su da su kama hanyar Sham inda yace su bi ta yankin Abni cikin kasar Balqa’a dake Sham, sannan ya umarci Usama da cewa kabi ta hanyar da aka kashe Mahaifinka, sannan ku shafe makiiya da karfinku, na Nadaka ka ka zamo Kwamanda na wanna Runduna ku kai hari da sanyin safiya, ga mayakan da aka jibge a Abni, ku kawar da su, ku ci gaba da tura mayaka da sauri don ku sami labarin abokan gaba da wuri-wuri. Idan Allah Ta’ala ya baka nasara a akansu to sai ku dan huta ku tsaya anan sannan ka tura yan liken asiri masu bada rahoto gaba don kawo labarin abunda ke faruwa Amma sai ya kasance mayakan Sahabbai sukai ta sabawa umurnin Kwamandan su Usama da umarnin Annabi har rundinar bata motsa ba har Annabi SAWA ya yi wafati ba su bi umarnin sa ba.
Usama ya yada zango ya sanya sansanin rundunar a tafiyar farsakhi daya daga Madina, amma mutanen sun ki shiga cikin rundunarsa saboda tsanantar rashin lafiyar Annabi SAWA.
Lokacin da wannan labari ya isa ga Annabi, ya je masallaci yana cikin matsanancin jinya ya nemi mutane gabata subi rundunar Usama amma ina suka ki.
Haka Usama ya koma Madina wanda Abubakar da kan shi yana daya daga cikin wadanda suka ki bin wannan runduna, bayan yaga ya hau kan Khalifanci, ya sake shirya wannan runduna domin su tafi yaki Sham bayan sun yo yakin sun dawo madina da Ganima mai yawa.