A bana kuma a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan Arba'in, halartar
Majalisar Ahlul-baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) na wucin gadi da shugabannin
ta a Karbala, ya ba da dama ga masu addini da al'adu da masu fafutuka daga
sassa daban-daban na duniya don yin hulɗa da aiki tare da juna.
A tsakanin ranekun 10 zuwa 21 ga watan Safar, an gudanar da taruka na musamman guda 12 a wurin taron majalisar Ahlul-Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, kusa da hubbaren Sayyidina Abul Fadl-Abbas, a Karbala, da dai sauransu. fiye da baƙi 1,600 daga kimanin ƙasashe 30 kamar Najeriya, Lebanon, Siriya, Kuwait, Tunisia, Palestine, Comoros, Yemen, Rasha, Azerbaijan, Turkey, Tajikistan, Afghanistan, Pakistan, India, Indonesia, Malaysia, Japan, Myanmar, Ingila, Portugal, Amurka , Netherlands, Faransa, Denmark, Bosnia da Herzegovina, Serbia, Kosovo, Montenegro, Albania da Uruguay suka halarta.
Shi ma Ayatullah Riza Ramazani babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya yi tattaki zuwa kasar Iraki a daidai lokacin tattakin Arba'in din Imam Husain As, kuma baya ga halartar tattakin Arba'in ya tsaya a Karbala, kuma a kan haka wani gungun malamai da masana na duniyar musulmi suka gamu da shi suka tattauna.
Abin da kuke karantawa shi ne hirar da kamfanin dillancin labaran Abna ta yi da Ayatullah Raza Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul-baiti (a.s) ta duniya dangane da bangarori daban-daban na gudanar da aikin ziyarar Arbaeen da kuma ayyukan da ake gudanarwa na wannan majalissar a cikin wannan taro na kasa da kasa a gefen ziyarar Arbaeen:
Abna: Da sunan Allah, Mai rahama. Gaisuwa da girmamawa. Muna farin cikin gabatar da wannan tattaunawa a kusa da hubbaren Sayyidush –Shuhada (a.s.) da Sayyidina Abul Fazl al-Abbas (a.s) a lokacin Arbaeen Husaini. Muna godiya ga Allah da wannan ni'ima. Don fara tattaunawar zamu so ku gaya mana yadda kuke ganin wannan mahanga ta addini da ta Arba'in da yadda ya kamata masu tunani su bayyana wannan ra'ayi. Bari mu fara tattaunawa game da Arbaeen kanta da kuma abubuwan da ke tattare da shi sannan mu ci gaba tare, muna cikin hidimta maku.
اعوذ بالله من الشیطان الرجیم. بسم الله الرحمن الرحیم. الحمدلله رب العالمین و صلی الله علی محمد و آله الطاهرین.
Ina neman tsari da Allah, daga Shaidan tsinanne. Da sunan Allah, Mai rahama mai jin kai. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Muhammad da alayensa tsarkaka.
Muna kuma godewa Allah mai girma kan gabaki dayan ni'imominsa ni’imominsa da ba mu sani ba da wasu daga cikin ni'imomin da muka sani amma ba za mu iya godewa ba, furucin Abu Abdullah (AS) a cikin Adduar Arafa cewa; Idan da ace zamu so yin godiya ga daya daga cikin ni’imomin Allah a dukan rayuwarmu, da “ ba zamu iya ba”; Ba za mu iya ba kuma idan wani yana so ya ƙidaya ni’imar Allah, “ba ta da iyaka”; Ba ma iya kirga lissafin falalarsa kuma wannan yana da matukar muhimmanci don haka ya kamata mu kasance masu godiya ga Allah a kowane lokaci, musamman wannan babbar ni'imar Arba'in da ya yi mana ba mu taba tunanin za mu samu irin wannan yanayi ba a Karbala inda har zamu samu damar yin tattaunawa game da Arbaeen. Yayin da ku kai yi nazari kan tarihin sashen Arba'in, zaku samu wannan yana daga cikin ni'imomin da babu wanda zai yi tunaninsa, sai Imamai Ma'asumin (a.s) da wannan ilimi na Ubangiji wadanda suke ganin abin da zai faru nan gaba, amma a gare mu, irin wannan abu ya kasance wanda ba za a iya hararo shi ba.
Batu na farko shi ne cewa Arbaeen ya samo asali ne daga wani babban lamari ne, wanda ya faru bayan wafatin Manzon Allah (SAW) shekaru 50 da suka gabata. Tabbas dangane da me ya sa za a yi magana dalla-dalla dangane da shi yana a mahuallainsa, me ya sa bayan shekaru 50 da wafatin Manzon Allah (SAW) aka soke kan jikan Manzon Allah (SAW) a saman mashi, ko kuma me yasa bayan shekara 30 bayan wafatin manzon Allah wato Alqur'ani mai shiru aka daga shi akan masuka, Alqur'anin da aka saukae daga sama. Wadannan binceke na tambayoyin shari'ar ya kamata a bincikesu a muhallansu.
To bayan haka a wannan yanayin Arbaeen da suka cewa tun daga ranar Ashura zuwa kwana 40, to yanzu zan yi bayani dangane da Arbain din, sannan zan koma kan wannan lamari.
Idan ana son yin nazari akan waki’ar Ashura, wannan waki’ar ta samo asali daga wasu manya-manyan abubuwa guda biyu na tarihi da suka gabata, daya shi ne manzancin Manzon Allah (SAW), wannan lamari mai girma da ya faru a tarihin dan Adam na aiko Manzon Allah (SAW). Wannan lamari mai mahimmanci ya faru ne don magance jahiliyya, don magance jahilci da kuma magance kowace irin tabarbarewa. A wancan lokacin, babbar tabarbarewa ita ce tabarbarewar akida, tabarbarewar tunani da nazari, tabarbarewa a fagen aiki da makamantansu, baya ga tabarbarewar siyasa da tattalin arziki, za ka ga duk irin wadannan rikice-rikicen da tabarbarewar da suka faru a lokacin aiken Annabta. Kamar su Labarin fadar Kisra da ire-iren su da wadannan sun faru ne a daidai lokacin da aka haifi Annabi (SAW) sannan kuma abin da ya faru na aike mai girma da ya faru, dukkansu ya kamata ako wane wannan mahallinsu a yi magana daki-daki.
Babban abin da ya faru kafin Ashura shi ne waki’ar Ghadir. Ghadir kuma yana daga cikin manya-manyan al'amura, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce akan Idul Ghadir: «أکبر أعیادی أمتی» "Mafi girman bukukuwan al'umma"; Babban Idin Al'ummata shi ne Idin Ghadir, wanda a zahiri ci gaba ne na wannan Sakon da aiken manzanci Menene ci gaban aike da sakon Annabta? A cikin bayani da tafsirin ayoyin Ubangiji. Domin Manzon Allah (SAW) shi ne ma’abuci mai bayyana addini:
«لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ ما نُزِّلَ إِلَيْهِمْ» (النحل: ۴۴)
“Domin ka bayyanawa wa mutane abunda aka saukar zuwa gare su” (Al-Nahl: 44). Wanda ya kasance majibincin addinin Ubangiji, majibincin Shari’a, kuma majibincin wahayi, shi ne Manzon Allah da kansa. Bayan haka, labarin Ghadeer shine kiyaye duk waɗannan nasarori da sakamakon Aiken Annabta. Wato fassarar Musulunci da Ahlul Baiti (a.s) suka gabatar ita ce fassara mafi inganci, cikakkiya kuma mai zurfi wanda ya samo asali daga wahayi da ilimi na Ubangiji. Wannan lamari ne mai matukar muhimmanci kuma lamari na uku shi ne irin waki'ar Ashura. Tabbas, wani babban lamari zai faru kuma shine Lamarin Mahdawiyya. Don haka wadannan hudun suna da alaka ta kud da kud da juna: Aiken Annabta, Ghadir, Ashura da Mahdawiyya. Wannan batu ne mai matukar muhimmanci.
Amma abin da ya faru a Ashura shi ne, mutane sun karkatar da addini, wato sun koma Jahiliyya. Wasu adadi na gungun mutane zamo su ne jagaban wannan addinin wanda basu da wani Imani da ilimi akan addini, Wanda aka dora akan wannan mukami wani mutum ne mai suna Yazid, mashayi ne, mazinaci, mai wasa da birrai, kuma aka danka masa masarautar musulmi a hannunsa a amatsayin amana. Idan aka yi la’akari da yanayin kasa na wancan lokacin, za ka ga cewa, alal misali Iran ta kasance wani bangare ne na waccan masarauta da gwamnatin Musulunci, don haka a irin wannan yanayi yanayin Musulunci da na kasashen musulmi ya na da fadi da yawan gaske. Kuma sai ya zamo hakan Masarauta da gwamnati Ta fada hannun wanda bai cancanta ba.
Bayan rasuwar Mu’awiya, ya ce a nemi wasu mutane su yi wa Yazidu mubaya’a, daya daga cikinsu shi ne Imam Husaini (AS). A lokacin da sarkin Madina ya gabatar da wannan shawara, labari ne dalla-dalla, ba ma son ambatonsa. Imam Husaini (a.s.) yana cewa: "Kamata Ba Ya Yiwa Irinsa Mubayi’a"
«و مثلی لا یبایع مثله»؛
Mu daga iyalan wahayi mu ke, danginsu iyali ne kaskantattu kuma ta fuskacin asali suna da tushe mai duhu, don haka wanda yake cikakken haske ba ya taba yin mubaya'a ga wanda yake da cikakken duhu. "Kuma misali na ba ya yiwa misalinsa mubayi’a" Idan har aka damka Musulunci amana a hannun irin wannan Fajirin to "karshen musulunci ya zo" «و علی الاسلام السلام», wannan abin al'ajabi da ya faru, wanda yake da matukar muhimmanci.
Imam Husaini (a.s) yana cikin wani yanayi na musamman da zai yi mubaya'a ba kuma ya tashi daga Madina zuwa Makkah a ranar takwas ga watan Zul-Hijja don kiyaye dakin Ka'aba, kiyaye Zamzam da Safa, kiyaye dukkan abubuwan tunawa na musulunci, kiyaye Imani da dukkan abunda annabawan Ubangiji suka samar suka bari na wannan babban gadon annabawa da Annabci, sannan ya bar Makka ya nufi Kufa, sannan a cikin wadannan yanayi na musamman, waki’ar Karbala ta auku; Anan zaka iya riska da samun hikimar yunkurin Imam Hussain As.
Waɗannan batutuwa suna da haɗaka da batutuwa waɗanda ke taka rawa wajen fahimtar muhimmin batu a cikin tushen ilimi. Sanannen abu ne kuma shine hakikanin gaskiya cewa Tushen Musulunci shine Annabi Muhammad (SAW), Kuma Wanzuwar Musulunci Ya samu ne da Imam Husaini (AS). Wannan magana ta shahara kuma faxin Manzon Allah (SAW) da ya ke cewa: “Husain Ni Ne, Ni Ma Husain Ne”
«حسینٌ منّی و أنا من حسین»
Haduwar ta kai gwargwadon haka Matsayin Sayyidina Abi-Abdullah (a.s.) ya zama wani gagarumin matsayi, wanda shi ne farfado da addini da raya sunnar Ubangiji. Imam da kansa ya yi nuni da cewa, a qarshe na fito ne domin neman gyara a al’ummar kakana:
«إنما خرجتُ لطلب الاصلاح فی امة جدی و أبی علی بن ابیطالب و اسير بسیرة جدی و علی بن ابیطالب(ع) »
“Tabbas Ba don komai na fito sai domin gyara a al’ummar Kakana da Babana Abi Ali Dan Abi Talib kuma nabi tafarkin Kakana da Ali dan Abi Dalib (As)”, sannan ya ce: “Domin An kasha Sunna an kuma raya bidi’a” «فإنّ السنة قد أمیتت و بدعة قد أحیی»؛; An lalatar da sunna, an rayar da bidi'a, kuma babu wani abu da ya rage a cikin addini na mulki da abin da ya kunsa, wato addini a zahiri an yi izgili da shi, wanda hakan shi ma daga mutumin da shine ke mulkar musulmi….
A tarihin rayuwar dan Adam bamu da Arba'in ba, wannan Arba'in ne kawai muke da shi. Tabbas Arbaeen yana cikin fagen suluki cewa «مَنْ أَخْلَصَ لِلَّهِ أَرْبَعِينَ صَبَاحاً ظَهَرَتْ يَنَابِيعُ الْحِكْمَةِ مِنْ قَلْبِهِ عَلَى لِسَانِهِ» "duk wanda ya kebanta da bautar Allah tsantsa har tsawon safiya 4o magudanan hikima zasu bayyana a zuciyarsa da harshena", ko misali ya zo a cikin hadisi cewa; Babu wata zuciya, sai dai idan tana da labule guda 40, ko kuma, a cikin bahasin Akhlaq, mun samu game da Sayyidina Musa (AS) cewa; “Kuma mun cika masa da kwana goma, sai ya zamo lokacin ganawarsa da ubangiji ya darare 40” (A’araf: 142).
«وَ أَتْمَمْناها بِعَشْرٍ فَتَمَّ ميقاتُ رَبِّهِ أَرْبَعينَ لَيْلَةً» (الاعراف: ۱۴۲).
Wannan wasu bincike ne na daban, amma ba mu da Arbaeen wato bayan wafatin wani da kuma bayan shahadar wani, sai akan wannan batu na shahadar Imam Husain As. kuma wannan shine al’amari kwara daya kawai, kuma a nan ya zama dole a binciki dalilin da ya sa aka yi haka da kuma dalilin da ya sa bayan wannan kissar Ashura suka yi ta kokarin kawar da wannan labari kuma suna ma kokarin ganin kabarin Imam Hussain (a.s.) bai wanzu ba ko kadan? Wannan ya faru sau da yawa a lokacin Khalifan Abbasawa Mutawakkil, Sun yi ƙoƙari sosai domin hakan ta faru, har ma don hana Ziyara, sun sanya jami'ai da yawa domin ya zamo mutane a yau da kullun ba su iya zuwa Ziyarah ba.
Mun samu wani darasi na musamman na tarihi wajen kiyaye wannan gado na Arba'in, wanda ya faro daga sahabbai kansu da sahabbai da daliban Imamai Ma'asumai (AS) na musamman har zuwa ga malamai. Malamai sun yi gagarumin yunkuri na farfado da Arbaeen kuma sun gudanar da shirye-shirye ta wannan hanyar a tsawon shekara. Sau da yawa a cikin wannan shekara dattijai da malaman addini da manyan malamai na makarantar hauza ta Najaf sun tafi Karbala da kafa, saboda muna da wasu hadisai game da muhimmancin da falala tafiya zuwa Karbala...