Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa: an gudanar da tattaki na barranta daga ma'abuta girman kai a
lokaci Arba'in na wannan shekarar tare da nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da ake
zalunta a Karbala Madaukakiya
a yammacin Lahadi 25 ga watan Agusta wanda yayi daidai da ranar Arba'in din shahadar Imam Husaini. Wannan tattakin dai ya samu halartar kungiyoyin jama'a daga
kasashe daban-daban da kuma jawaban 'yan gwagwarmaya daga kasashen Iraki, Labanon, Tunisiya da kuma Yemen.








































































