16 Agusta 2024 - 18:09
Shaharar Tattakin Arbaeen Ta Yadu A Duniya| Yadda Kafofin Sadarwa Na Duniya Ke Mamakin Yawan Miliyoyin Al'umma A Taron Arbaeen + Hatuna

Ziyarar Arba'in wani lamari ne na ta'aziyya ga iyalan gidan manzon Allah (S.A.W) kuma ana daukarsa a matsayin daya daga cikin muhimman ayyukan ibada na shi'a da ya zama babbar ibada da ke kusanto da junan zukatan dukkan masoya Imam Hussaini (AS) daga kasashe daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya kawo maku rahoton cewa: a ranekun tarukan Arbaeen na shugaban shahidai Aba Abdullahil Husain (a.s) tare da halartar miliyoyin maziyarta Sayyidush-Shuhada (AS) a tattakin Arbaeen, Kamfanin Dillancin Labarai na Abna ya gudanar da tattaunawa da Malamai da wasu Masana game da muhimmancin wannan aikin ibada na ziyara d atattakin Arbaeen.

Tattaunawar da ke tafe kamfanin ya gudanar da ita ne tare da Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen Sheikh Muhammad Jabbar Mansur Al-Bahadili daya daga cikin malaman lardin Maysan na kasar Iraki, wacce ta shafi bangarori daban-daban na tattakin Arba'in, wadda ta askance kamar haka:

ABNA: Da Farko Za Mu So Ku Gabatar Da Kankau A Taqaice, Sannan Ku Yi Takaitaccen Bayani Dangane Da Falala Da Matsayi Na Raya Arbaeen Imam Husaini A Mazhabar Shi'a.

Da sunan Allah, Mai rahama Mai Jin Kai

بسم الله الرحمن الرحيم

Muna cikin lokacin da ya dace da tattaki na Arba'in da dawowar sauran iyalan Annabi (sawa) zuwa Karbala kuma muna magana ne kan wannan lamari mai muhimmanci da girma da yake a cikin al'ummar Musulunci a yanzu. Wannan gagarumin tattakin bai tsaya ga ‘yan Shi’a kadai ba; Amma dai wanda ya kafa shi shi'a ne, amma yau ya yadu a duniya.

Ni sunana Sheikh "Muhammad Jabbar Mansur Al-Bahadili" ne daga mutanen lardin Maysan na kasar Iraki, gundumar Maimunah. Na yi hijira zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shekara ta 1990 a lokacin yunkurin Shabaniyah, kuma na kammala karatun digiri a Darul Mu’alimin na kasar Iraki. Na shiga makarantar hauza a 1991 kuma na kai ga matakin Durusu Kharij. A halin yanzu ina karatu a Kwalejin Shahid Sadr da Jami’ar Ahlil-Baiti (As), kuma bayan na samu digirina na farko da na biyu, a halin yanzu ina karatun digiri na uku. Na yi tafiya zuwa Lebanon, Saudi Arabia, UAE da kuma Sweden. A kasar Sweden, na shafe shekaru bakwai ina jagorantar Sallar Juma'a a Majalisar Ahlul-Baiti (AS) da ke Stockholm kuma na yi wa'azi a garuruwa daban-daban na kasar Sweden.

Allah Ta’ala ya shar’anta tafiya aikin Hajji zuwa Baitul-Haram kuma ya sanya sunna mai daraja ta raya ibadar tafiya zuwa Bait-Allah-ul-Haram a cikin rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama. Ya shahara dangane da Imam Hasan Mujtabi (amincin Allah ya tabbata a gare shi) cewa ya yi aikin Hajji sau 20 tare da cikakkiyar takawa da kafa.

Ana iya kira aikin ziyarar Imam Husaini (a.s.) da Hajjin Husaini, domin ya zo a cikin hadisai cewa Ziyarar Husaini (a.s.) ya na daidai da Hajji dubu ko Hajji dari ko umra dari; Har ma ya zo a cikin ruwaya daga Annabi (SAW): Duk wanda ya ziyarci dana Husaini (AS), za a rubuta masa aikin Hajji da Umra. A cikin "Kamiliz-Ziyarat" Marigayi Qulwaih ya kawo hadisai masu daraja na Manzon Allah (SAW) da Amirul Muminin (a.s) da Ahlul Baiti (A.S) dangane da muhimmancin ziyarar Imam Husaini (AS) da kuma cewa ziyarar Imam Husaini (AS) a kowace rana da kowace Juma'a da kowane wata yana da lada mai yawa. An kawo nau’ika da dama na ziyarar Imam Husain (a.s), kamar yadda aka kawo addu’o’I da suka kebanta da sha’aban da Rajab da Ramadan har ta kaiga mun isa zuwa Idin Fitr da Idin Adha.

A cikin hadisin “Sudair Sairafi” ya zo cewa Imam Sadik (a.s) ya tambayi Sudair cewa: “Sadair, kana ziyartar Imam Husaini (AS) kowace rana ko kowane mako ko kowace shekara kuwa? Sai Sudair yace ina tsoron zaluncin masu mulki. (Azzalumai sun yaki Imam Husaini (a.s.) kuma za mu yi bayani kan irin zaluncinsu. Imam Sadik (a.s.) ya ce wa Sudair: Ka hau rufin gidanka ka dubi bangaren dama da hagunka ka ce: السلام علیک یا اباعبدالله،  السلام علیک و رحمة الله وبرکاته, idan ka yi haka, za a rubuta maka ladar "Zurah" guda daya wanda (Zurah) guda daya yana daidai da Hajji da Umra daya.

Akwai hadisai da suke jaddada cewa: Ziyarar Imam Husaini (a.s.) tana kara shekrun rayuwa da wadata, kuma bisa ruwayar Imam Sadik (a.s.) ana bayar da mafi karancin lada ga maziyarcin Imam Husain (As). Ta hanyar "Kare dukiya, rayuwar mai ziyarar da ta 'ya'yansa". Daga cikin ayyukan ziyarorin Aba Abdullahil-Husain (a.s) har da ziyarar Ashura, wanda ita ce ne tushe na mahadar Musulunci kuma fitilar akidar Ahlul Baiti (a.s.) da yaduwar gaskiya a doron kasa.

A yau, hatta kafafen sadarwa na duniya suna mamakin tattakin masu ziyarar Arbaeen din Imam Husain (a.s.); Ziyarar Arbaeen, musamman a shekarun baya-bayan nan, ta zama wani abin tarihi da daukar darasi ga dukkan mutane.

Wannan gaskiya ta fara bayyana irin soyayyar da mutane suke yi wa jikan Manzon Allah (SAW) sannan ta bayyana zaluncin da aka yi wa Ahlul Baiti (a.s.) Ta'aziyyar ziyarar Arba'in tana daya daga cikin muhimman ayyukan ibada da suka zamanto babbar ibada da ke kusanto da junan zukatan dukkan masoya Imam Hussaini daga kasashe daban-daban.

 * Ku Dan Yi Mana Bayani Dangane Da Tarihin Taron Arbaeen.

A yau, Ziyara da tattakin Arbaeen da yawo ya zamo abun halartar miliyoyin Al’imma. Tambaya anan ita ce, wane ne farkon maziyarcin Arbaeen? Idan muna so mu koma ga hadisai, za mu ga cewa farkon wanda ya tafi Karbala da kafa don ziyarar Arba’in kuma ya hadu da Ahlul Baiti (a.s) shi ne Jabir bin Abdullah Ansari; Yayin da ya ji labarin shahadr Aba Abdullahil-Husain (a.s) sai ya garzaya ya ziyarci Imam Hussaini (a.s) tare da bawansa "Atiyyah Aufy" bayansa Imam Sajjad (a.s) ya zama maziyarcin Arbaeen na Imam Husaini As.

A ginin "Abdul-Razzaq Muqram", akwai wasu gungu da su ka tfaki akan cewa Ahlul Baiti (AS) ba su koma Karbala ba a wannan shekarar. “Maraddir-Ru’uss” na nufin mayar da kawunansu zuwa ga tsarkakakku jikkunansu da kuma binne su da Imam Zainul Abidin (a.s) ya yi. Wasu jama'a daga kasar Yemen da sauran wasu jama'a sun shiga wannan yankin kasar domin gudanar da ziyarar Arba'in, amma tafiyar tattakin Arbaeen ta shahara ne tun zamanin Imam Sajjad (a.s).

 A lokacin daular Usmaniyya, maziyarta Imam Husaini sun kasance cikin hadari. Wasu daga ciin makiya Nasibiwa na Bagadaza suna cutar da mabiya Ahlul Baiti (AS); To amma yanzu idan muna so mu kalli aikin ziyarar Imam Husaini (AS) a matsayin wani sauyi, zamu ga halartar wadannan miliyoyin mutane ya faro ne bayan faduwar hukumar Saddam Husain.

Hukumar Saddam da gwamnatinsa ta Ba'athi, wadanda a hakikanin gaskiya sun kasance Nasibawa ne, sun kasance masu adawa da Imam Husaini (a.s.) da ‘Yan Shi'ar Husaini, mutane sun kasance suna zuwa Ziyarar; Amma gwamnati ta yi ta yin kisa tare da kawar da maziyarta da dama a kan hanyar zuwa Karbala; Tabbas wadannan laifuffukan ba sabon abu bane ga Ba’asiyawa, domin Ba’asiyawa sun koyi wadannan laifukn ta’addcin ne daga Banu Umayya da ‘ya’yan Banul Abbas.

Hatsarorin da suka fuskanci maziyarta Imam Husaini (a.s) a zamanin mulkin Ba’ath, sune dai irin wadandan hatsarorin da aka fuskanta a lokacin halifancin Mutawakkil Abbasi. Domin kuwa a zamanin Mutawakiul Abbasi, su na yanke hannuwa da kafar masu ziyara ne, suna karbe kudi da kashe maziyarta don kawai mutane su kaurace tare da nisantar ziyarar Imam Husain (a.s.). Amma shauki da soyayyar ga Imam Husaini (a.s) shi ne abin da ya kira mutane zuwa ga yin wannan gagarumin aiki na sadaukarwa dominsa, ta yadda idan har sun kai ga matsayin shahada Allah Ta’ala ya yarda da su baki daya.

Ya kamata a lura cewa aikin ziyarar Arbaeen bai takaitu ga Najaf da Karbala kawai ba. "Ra’asul-Baishah" yanki ne na kan iyaka kuma yanki mafi nisa a Faw, inda mutane ke tafiya zuwa Karbala mai tsarki daga cen; duk da mutanen a farko suna zuwa ziyarar Amirul Muminin (AS) sannan su je ziyararshugaban Shahidai Imam Husain As.

 A yanzu dai za ka ga bunbutowar miliyoyin daga kowane bangare zuwa ziyarar Aba Abdullahil-Husain (AS), don haka sai ya zama cewa wannan tattaki na da dadadden tarihi. Tun daga zamanin daular Usmaniyya, da zamanin Baathiyyah da zamanin ISIS da kuma kafin ISIS, maziyarta Imam Husaini (a.s.) a kodayaushe suna cikin hatsarin gaske kuma har ta kai sun yi shahada; Amma sun kasance suna cewa rayukanmu hadaya ce ga matsayin Imam Husaini. Don haka mu ba da jini da yin shahada don wannan ibada mai albarka.

* Menene Nasihohinku Da Shawararku Ga Masu Tawagogin Da Masu Ziyarar Arbaeen Din Imam Husaini As?

Ina so in ce wadannan masu yin Hidima; Ma'abuta Maukibobi da ma'abota Husainiyoyi da gidajen sauka da masallatai da tantuna da suke dukkan lardunan kasar Iraki, dukka ba shakka kowane yanki ya sha bamban da sauran yankuna. Amma wannan kyakkyawan taryar baƙin yana haɗa zukatan masu yin hidimar ne. Zukatan masu hidima suna cike da farin ciki, jikinsu yana yana da ƙarfi kuma ba su yin barci sai dan kaɗan, dole ne bayyana cewa waɗannan ayyukan hidimar ba ayyukan gwamnati ba ne.

Al'ummar kasar Iraki bayan kammala aikin ziyarar Arbaeen, suna tattara kudade don gudanar da tarukan Arba'in na shekara mai zuwa, suna tunanin abin da za su bayar don yi wa maziyarta Imam Husain (a.s.) hidima. Don haka, don Arbaeen na shekara mai zuwa, suna tanadar asusu don tattara kuɗinsu.

* Menene Matsayin Malamai Dangane Da Gudanar Da Tattakin Arbaeen? Kuna Da Wani Abu Da Zaku Iya Tunawa Game Da Arbaeen?

A cikin tarihin rayuwar shahararrun malamanmu da suka gabata, an ambaci cewa manya-manyan maraji’oi sun kasance suna ziyartar Imam Husaini (a.s) tare da dalibansu. Wasu kuma suna ziyartar Imam Husaini (a.s) a kowane dare, sannan suna tafiya Karbala daga Najaf ta Tariqul Ulama.

Muna da wata Husainiya wanda ake raba ruwa a cikinta a kwanakin Arba'in; A wani tattaki da na yi kusan tsayin mita 1000 a hanyar, na isa Maukibin Basra, sai mai kula da maukibin yayi min tayi abincin rana, amma na ce na ci abinci. Ana cikin haka sai wani Kurma ya yi min nuni da, ya ce in shiga Maukibinsu su, sai wani daga cikin mutanen da ke wurin ya ce da ni: Kada ka karya zuciyar wannan Beben! Sai na shiga Maukibin na su, bayan ganawar da muka yi da masu maukibin, sai ga Beben ya yi magana, na tambaye shi: kaifa ka kasance bebe ne? Yaya ka yi magana? Ya ce idan ban yi haka ba maziyarta ba za su shiga Maukibin nawa ba.