Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya ta fitar da sanarwa tare da yin Allah wadai da kisan da aka yi wa mabiya Shi'a a Parachenar kasar Pakistan.
Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku cewa, Majalisar Ahlul-baiti (AS) ta fitar da wata sanarwa tare da yin Allah wadai da kisan da aka yi wa mabiya Shi’a a birnin Parachinar na kasar Pakistan.
Bayanin na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya ya zo kamar haka;
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai
Lallai Mu Daga Allah Mu Ke Kuma Gareshi Mu Masu Komawa
بسم اللَّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ
انا لله و انا الیه راجعون
«وَمَن یَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُّتَعَمِّدًا فَجَزَآؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِیهَا وَغَضِبَ اللّهُ عَلَیْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِیمًا»( نساء 93)
"Kuma wanda ya kashe mumini da gangan, to sakamakon shi ita azabar wutar Jahannama yana mai dawwama acikinta kuma fushin Allah ya tabbata a kansa, kuma ya tsine masa, kuma ya tanadar masa da azaba mai girma". (Nisa'i: 93).
A wannan karon ma shahadar 'yan shi'a cikin zalunci a yankin Karam Agency (Parachanar) na kasar Pakistan, ya sanya bakin ciki a zukatan dukkanin 'yan shi'ar duniya da musulmin Pakistan. Wannan mataki da kungiyoyin takfiriyya suka aiwatar wanda ya yi sanadin shahadar mutane sama da 35 tare da raunata kusan 'yan Shi'a 160, ya sake bayyana irin zaluncin da ake yi wa 'yan Shi'a da al'ummar wannan yanki wanda hakan zai sanya kasashen duniya kara kaimi wajen sanin wannan yunkuri na Takfiriyya tare da fuskantar sa da yakarsa.
Ko shakka babu, kokarin hana tashe-tashen hankula na cikin gida da na kabilanci a tsakanin al'ummar yankin Parachenar, da magance matsalar fatara da ta'addanci, kokarin hadin kan Musulunci na daga cikin batutuwan da ya kamata musulmin Pakistan da kasashen duniya su kara mai da hankali a kai.
Majalisar Ahlul Baiti (A.S) ta duniya ta yi kakkausar suka ga wadannan ayyukan takfiriyya tare da nuna goyon baya da tausaya wa wadanda suka tsira da rayukansu da kuma jajantawa al’ummar musulmi da mabiya Ahlul-baiti (A.S) na kasar Pakistan tana mai rokon Allah cewa; Allah madaukakin sarki ya jikan shahidan da wannan rigingimu ya ritsa da su.
Har ila yau, yayin da take gode wa gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Pakistan kan kokarin da take yi na tunkarar takfiriyya da kungiyoyin 'yan ta'adda, ta yi kira da ta kara himma sosai wajen tunkarar masu ta'addanci da kare rayuka da dukiyoyin 'yan Shi'a a wannan yanki.
Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya
24 Muharram 1446