Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Mutanen da aka kama sun bayyana a cikin ikirari cewa suna shirin aiwatar da kisan kai a yankin Saravan bisa umarnin ƙungiyoyin 'yan ta'adda da maƙiya.
A ci gaba da atisayen "dakarun Shahidain Tsaro 2", sun gano wata ƙungiyar 'yan ta'adda da ta aikata ayyukan ta'addanci da dama a yankin Saravan a cikin shekarar da ta gabata kuma an kama su ta hanyar ayyukan leƙen asiri.
Your Comment