30 Disamba 2025 - 18:26
Source: ABNA24
Najeriya: Abun Fashewa Ya Tashi A Asibitin Kebbi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa wani abin fashewa ya tashi a Babban Asibitin Bagudo da ke jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya afku ne a safiyar yau Talata a cikin asibitin, tare da cewa ba a samu asarar rai ko ɗaya ba.

Abin da ya faru a babbar asibitin Bagudo da ke Birnin Kebbi abin tayar da hankali ne matuƙa, domin asibiti wuri ne na jinƙai da ceto rayuka, ba filin rikici ba. Duk wani hari a irin wannan muhalli na karya ƙa’idar ɗan’adam, kuma yana ƙara tsoratar da al’umma fiye da kima.

Your Comment

You are replying to: .
captcha