16 Yuli 2024 - 15:06
Ranar Karbala 10 Ga Watan Muharram Shekara Ta 61h Ranar Kukan Bakinciki Da Zubar Hawaye Ga Dukkan Halittu Na Gar-Garu

Ranar Da Aka Kashe Dan Manzon Allah (SAWA) Da Iyalansa Da Sahabbansa Tsarkaka A Filin Karbala Ranar Da Dukkan Halittu Masu Imani Su Kai Kuka Sammai Da Kassai Sukai Ruwan Jini.

Wannan rana rana ce da ta shahara a shekara, rana ce da ba’a mantawa da ita a tarihin ɗan adam. Domin Abubuwa Masu girma sun faru A wannan babbar rana, wanda ko ya fisu girma tare da share tasirin sauran shine aukuwar Shahadar Imam Husian As da Mataimakan sa don kare tare da raya wannna Addini wadda yake an nuna haƙuri, sadaukarwa da Jajircewar gungun mutane da sukai Imani da Allah suka tsaya a gaban tarin makiya Mafiya laifi da zunubai a duniya. Wannan rana ita ce ranar sadaukarwar Imam Husaini (as) da sahabbansa masu aminci kuma za tana kasance na su har abada. A wannan rana, muhimman abubuwa sun faru a ƙasar Karbala, wanda har abada za a rubuta su a tarihin ɗan adam.

Anan zamu kawo a taƙaice muhimman abubuwan da suka faru a ranar Ashura a shekara ta 61 bayan hijira:

 

1- Shirya Runduna:

            Imam Husaini (as) Bayan sallar asuba, ya raba karamar rundunarsa, wacce ta kunshi mayaka mahaya doki 32 da mayaka na kasa 40, zuwa rukuni uku. Ya sa rukuni na farko a sashin dama bisa jagorancin Zuhair ibn Qain, rukuni na biyu a ɓangaren dama bisa jagorancin Habib ibn Mazahir, da kuma rukuni na uku a tsakiyar su ƙarƙashin jagorancin Imam Husain As. Ya kuma mika tutar rundunar ga dan uwansa Sayyiduna Abbas Ibn Ali (as) sannan ya sanya sojojinsa a gaba da tantunan su.

            Shi ma Umar dan Sa'ad ya sanya jagorancin rundunar rukunin damar sa ga Amr bn Hajjaj, ta hagu kuma ga Shimr dan Dhi Al-Jushn, ya sanya jagorancin mahaya doki ga Orwa dan Qays, jagorancin mayaka na kasa kuma ga Shabbs dan Rubi'i, kuma ya mika tutar sojojin sa ga bawansa Duraid.

 

2- Nasiha Da Wa'azin Imam Husaini (As) Ga Wannan Runduna:

            Kafin a fara yaƙin, Imam Husaini (a.s) yayi nasiha da janhankali ga rundunar kafirai ta makiya ta hanyar yin wa’azi domin wayar dasu, ya kirasu ga kwantar da hankalinsu da gujewa  zubar da jini da yin faɗa. Baya ga kansa, Imam ya aika wasu daga cikin sahabbansa zuwa ga rundunar Umar bn Sa’ad a wannan rana, domin ya zamo ko ta hannun su wadannan runduna sun shiriya su dawo.

Wanda ya zamo daren a ashura mayaka 22 daga rundunar Umar dan Sa’ad suka bar sansanin su suka koma ga rundunar Imam Husain As.

 

3- Nadamar Hur Dan Yazid

            Hur dan Yazid wanda yana daya daga cikin kwamandojin rundunar Umar da Sa'ad kuma daya daga cikin Larabawa masu jaruntaka da jajircewa, ya yi nadama a ranar Ashura kafin fara yakin ya koma rundunar Imam Husaini (as).  Duk da cewa shi ne mutum na farko da ya tare wa Imam Husaini (as) hanya tare da anfani da karfi ya tilastawa Imam Husain bin hanyar Karbala, amma Aba Abdullah Al-Hussein (as) ya karbe shi kuma ya karbi tubansa, ya sanya a cikin sahabbansa.

Komawar Hur dan Yazid da wasu runduna ta Umar bn Sa’ad zuwa rundunar Imam Husaini (as) ya haifar da shakku da ruɗar wasu kafirai da yawa kuma ya haifar da wani abin mamaki a tsakanin rundunar Umar dan Sa’ad.

 

4- Kawo Farmakin Na Makiya Gaba Daya:

            Umar dan Sa'ad, wanda ya kasa jure komawar wasu mutane zuwa rundunar Imam Husaini (as), sai ya tara rundunarsa ya basu umurnin na kai hari gaba daya. Cikin kankanin lokaci, rundunonin biyu sun ya mutse tare da fara gwabza yaki.

Kowanne daga cikin sahabban Imam Husaini (a.s) ya yi yaki da dimbin makiya da kuma yaki na fito na fito , kuma ba a ga wani rauni ko ra zani a garesu ba, kuma wannan babbar jamrumta da imani mai karfi ya yi nauyi da wahalarwa ga makiya. A wannan yakin, an kashe kusan sahabban Imam Husaini (as) hamsin daga bangaren makiya kuma na kasha daruruwa.

 

5- Yakin Dai-Daikun Mutane Fito Na Fito:

            Maƙiya, dasu ka ga yakin mai gaba daya basu samu wata nasara ba sai suka koma ga yaƙin mutum daidai fito na fito. Domin duk da cewa gaba dayan rundunar Umar dan Sa'ad sun zo don yakar Imam Husaini (as) ne, amma a cikinsu akwai da yawa da ba su yarda da yakar 'ya'yan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa ba, kuma an masu tilas ne,. saboda haka, sunyi jinkiri da ja baya wajen yaƙin na mamaye da gaba ɗaya, hakan ya sanya Umar dan Sa’ad ya samu ci baya wajen cimma mugun nufinsa. A wannan mataki shima an kashe mataimaka Imam Husaini da dama.

 

6- Sallar Azahar Din Ranar Ashura:

            A cikin zazzafan yaki, Abu Sumama As-Saidawi ya tunkari Imam Husaini (as) ya ce masa lokacin dakatawa yayi. Imam Husaini (as), wanda yake bada muhimmanci na musamman ga Sallah, ya ba da umarnin a dakatar da yaki kuma kowa ya je yayi Sallah. Makiya wadanda ba su damu da sallar ba, cikin tsoro suka far ma Imam da sahabbansa yayin da suke sallah ta hanyar harba masu kibiya. Abdullahi Hanafi, wanda ya mai da kansa garkuwa ga Imam Husaini (as), ya sha harbi goma sha uku daga makiya, daga karshe ya shiga sahun masu haduwa da Ubangiji yana mai kare martabar Imam Husaini (as).

 

7- Shahadar Sauran Sahabban Imam Husaini (As).

            Bayan sallar azahar na Ashura, sauran sahabban Imam Husaini (as) sun yi shahada daya bayan daya. Zakunan jarumai kamar su Zuhair bn Qayn, Nafi'u bn Hilal, Muslim bn Awsajeh, Habib bn Mazahir, Hur ibn Yazid, Barir bn Khudair da jarumai maza daga Bani Hashim irin su Ali Akbar Abbas bn Ali Qasim bn Hasan, Abdullahi, Abdullah bin Muslim amincin Allah ya tabbata a gare su, da Wasu da suka taimakawa shugabansu, maigidansu Imam Husaini (as), duk sunyi Shahada a Hannun makiya Ahl -Bayt (as).

 

8- Fito Na Fiton Imam Husaini (As) Da Shahadar.

            Imam Husaini (a.s) bayan ya rasa dukkan sahabbansa, ya tara mata da yara a cikin tanti ya yi musu ta’aziyya ya umarce su da yin hakuri ya yi musu bankwana da karyayyar zuciya. Imam ya nada dansa Imam Zaynul-Abidin (as), wanda ke fama da matsananciyar rashin lafiya, a matsayin magajinsa, sannan ya yi bankwana da shi ya shirya yaki da abokan gaba. Imam Husaini (as) shi kaɗai ya yi yaƙin sa’o’i da dama da tarin makiya masu yawa, inda ya kashe da yawa daga cikinsu wasu kuma yaji masu ciwo.

            Imam da kansa ya sami raunuka da dama a fagen daga kuma a sakamakon haka, ya fado daga kan dokinsa "Zul-Janah" makiya kuma suka kai masa farmaki. Daga karshe, Shimr dan Dhi Al-Jaushan, cikin rashin tausayi da ke kekashewar zuciya, ya matso kusa da Imam dake cike da jini da rauni ya sare masa kan sa mai albarka, kuma ta haka ruhunsa mai daraja ya tashi zuwa sama.

 

Assalamu Alaika Ya Aba Abdullah Wa’ala Arwahillati Hallat Bi Fini’ik Alaikum Minna Salamullah Abadan Ma Bakina Wa Bakiyallailu Wannahar.

 

Damun samun cikakkakken bayani mai gamasarwa sai aduba wadanna littfa Insha Allah

Al’irshad, ( Sahukul Mufid) shafi na 447 da Alfutuh Na ( Ibnul A’asamul Kufy) shafi na 901 da Munhatal Ammal ( Shaiku Abbasul Kummy) J1 shafi na 342, Luhuf Sayyid Ibn Dawus shafi na 114.