A wannan rana wasu daga cikin
sahabban Imam suka yi kokarin tono rijiya. Labarin wannan al'amari ya isa ga
Ibn Ziyad kuma ya umarci Umar bin Saad da ya gaggauta dakatar da aikin hakar
rijiyar domin Imam Husaini (a.s) da wanda ke tare da shi su wanzu cikin jin
kishirwa. Umar Bin Saad ya kuma yi wa Sahabban Imam Husain Alaihi Salam
barazana da su cike rijiyar da kasa, idan ba haka ba sai ya kai musu farmaki.
Bayan sa'a guda, ƙishirwa ta yi kamarai a cikin ayarin Imam. Don haka ne Imam Husaini (a.s) ya umurci Sayyiduna Abbas (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da ya je ya samo ruwa ga mutanen tantunansa. Lamarin debo ruwa ya faru ne a cikin duhun dare, kuma tun daga wannan lokacin ne aka ba Sayyidina Abul Fazl al-Abbas, a matsayin Siqayah – wato mai shayar da ruwa-.
A rana ta takwas ga watan Muharram ne Ubaidullah bin Ziyad ya hau kan mimbarin masallacin ya yi jawabi ga jama'a domin karfafawa da kuma yi musu barazanar tsayuwa gaban Imam Husaini (a.s) don su yake shi. Ya sanar da cewa, duk wanda bai je Karbala ba a cikin wannan lokaci, bai kuma yi fada da rundunar Imam Husaini ba, to jininsa ya zama halal, kuma za a yanke masa hakkinsa daga Baitul-Mal.
Ana cikin haka sai yazid la’ananne ya aika da kudi dinari dubu hudu da dirhami dubu dari biyu zuwa ga Ubaidullah domin biyan kudaden soji na wannan yaki na zalunci. Ubeidullah La’ananne ya kuma baiwa wasu mutane dubu 25 kayan yaki domin yakar Imam Hussain (amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Madogara:
1- Nafasul Humum.
2- Al’iarshad; Sheikh Mufid.
3- Maqtal Imamul-Husain, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; Khwarazmi.
4- Maqtal Imamul-Husain, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; Bahrul Ulum.
5- Ayineh Dar Karbala; Muhammad Riza Sangri.
Abubuwan Da Suka Faru A Ranar 9 Ga Muharram 61 Hijiriyya
1- Zuwan Takardar Amincin Kariya Ga 'Ya'yan Ummul-Banin, Amincin Allah Su Tabbata A Gare Su.
A wannan rana Shimr la'ananne ya kawo wa Sayyidina Abbas (a.s.) da 'yan uwansa takardar amincewa....(1) Sayyidina Abbas (a.s) ya ce yana mai maida masa martani akanta da kakkausar murya: Allah ya tsine maka da shugabanka. Shin kun bamu Amanar tsira alhalin dan Manzon Allah bai tsira ba? (2)
2- Neman Jinkirta Yakin Daga Fuskacin Imam Husaini (A.S).
A yammacin Tasu'a an baiwa Imam (a.s.) wa'adin dage yakin har tsawon dare daya. (3) to Lokacin da Umar Sa’ad ya shirya rundunar yaki da Imam (a.s.) kuma ta tabbata cewa ya yi niyyar yakar shi, sai Imam ya ce wa dan’uwansa Abbas (a.s.) da ya nemi su jira zuwa bayan dare. Ba su karba ba da farko, amma sai suka yarda su jira dare guda (4).
3- Isowar Sabbin Sojoji Zuwa Karbala
A wannan rana wata runduna dauke da makamai ta shigo Karbala daga Kufa bisa umarnin Ibn Ziyad, kuma Shimr tsinannae ya kawo wasikar Ibn Ziyad (5).
4- Jawabin Imam Husain (AS) Ga Sahabbansa
A yammacin wannan rana ne Imam Husaini (a.s.) ya yi huduba a cikin sahabbansa, kuma Sahabbai sun bayyana amincinsu da dakewarsu a bayansa (6).
5- Sojojin Umar Dan Sa’ad Sun Fuskanci Wajen Da Tantinan Ima Husain As Su Ke.
Bayan dawowar Shimr, Umar Saad ya kira rundunarsa yana mai cewa: Ya ku rundunar Allah! Ku hai ababen hawanku kuma ku yi farin ciki zaku tafi zuwa Aljanna! Sai sojojin suka fuskancin inda tantunan Imam Husain As su ke. Sayyid Abbas ya zo wajen Imam ya ce dan'uwana sojojin sun fuskantoka.
Sai Sayyiduna Husain As yace: Abbas! Raina ya zamo fansarka, ka tambayi me ya faru da suka fuskanto mu? Sayyid Abbas ya zo wurin sojoji da mahayan dawakai guda 20, ya tambaye su me suke nufi, sai suka ce: “Umarni ya zo daga shugaba cewa ko ku yi masa mubaya’a, ko mu yake ku. Sayyid Abbas ya ce: Zan isar da sakonku ga Imam, in dawo. Sayyidina Husain As ya ce: “Abbas, ka ce su yi mana jinkiri a daren nan domin mu yi Sallah da neman gafara. Sayyid Abbas ya zo ya tsaya a gaban sojoji ya yi masu wa’azi ya nemi a yi masa jinkiri a wannan dare. Sai rundunar Umar Sa’ad ta koma inda suke, hakan kuwa ya faru da yammacin rana ta tara ga watan Muharram shekara ta 61 a filin Karbala.
Madogara:
1). I’ilamil Wara: Juzu'i na 1, shafi na 45
2). Az Madineh ta Madineh: shafi na 381-382
3). Bihar al-Anwar: Juzu'i na 44, shafi na 392
4). Manaqib Ibn Shahr Ashub: Juzu’i na 4, shafi na 107
5). Faizul-Alam: shafi na 146
6). Manaqib Ibn Shahr Ashub: Juzu’i na 4, shafi na 107.