Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA - ya habarta maku cewa: Kungiyar
gwagwarmayar Musulunci ta Hamas cikin wata sanarwa ta jaddada cewa munanan
shaidar fursunonin da aka sako da kuma irin munanan alamomin ayyukan da aka yi
a jikinsu, inda yanayin da wasu 2 daga cikin fursunonin da aka sako masu suna
kamar haka: "Mu’az Umaranah" "Dan jarida” da kuma “Mu'azzaz Ubaiyat”
wanda ya ke “Dan wasa” ne, ya nuna irin munanan laifuka da munanan ayyukan
azabtarwa da ke faruwa a gidajen yari da wajen da ake tsarewa na gwamnatin
sahyoniyawan.
A cikin wata sanarwa da aka bayar da kwafinta ga cibiyar yada labarai ta Falasdinu, wannan yunkuri ya yi nuni da cewa, shaidar da fursinonin "Mu'azzaz Ubayyat ya bayar game da halartar ministan 'yan ta'addar sahyoniyawa "Itmar Bin Gweir" ya nuna cewa irin mummunan ayyukan azabtarwar da wannan minista da sauran mambobin wannan gwamnatin sahyoniya tsattsauran ra'ayi su kayi gareshi sun sanya kamu da ciwon hauka?
Hamas ta tabbatar da cewa: Ayyukan mugunta da azabarwar da fursunonin mu ke fuskanta a gidajen yarin yahudawan sahyoniya sun ninninka fiye da wanda fursunonin suke fuskanta a gidajen yarin Guantanamo da Abu Gharib, kuma gwamnatin sahyoniyawa da sojojinta fasikai sun tattake dukkan yarjejeniyoyin kasa da kasa da dokokinta da suka shafi mu'amala da waɗanda aka kama.
Har ila yau, wannan kungiyar ta sanar da cewa, munanan mu’amalar gwamnatin yahudawan sahyoniyawan na bukatar shiga tsakanin gaggawa na kasashen duniya da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya da wasu rassanta, da kuma kafa kwamitoci da za su halarci wuraren da ake tsare da su tare da gudanar da bincike kan lamarin cin zarafi da ake yi musu, sannan a mika jami'an yahudawan sahyoniya ga tsarin shari'a na kasa da kasa saboda aikata laifukan yaki da kuma yi musu shari'a kan aikata wadannan laifuka.
A karshen bayanin nata, kungiyar Hamas ta bukaci al'ummar Palasdinawa da suke birnin Kudus da yammacin kogin Jordan da su tallafa tare da goyawa fursunonin Palasdinawa da taimaka musu har sai an kubutar da su daga gidajen yarin yahudawan sahyoniya da kuma 'yantar da wadannan fursunonin da kuma kasarsu da wurare masu tsarki daga sharrin sahyoniyawa ta hanyar kara karfin fuskantarsu ga sojojin sahayoniya.
Mummunan Halin Da Fursunonin Palasdinawa Ke Ciki Bayan An Sako Su
Mu’azzaz Ubayyat fursunan Palasdinawa da ke zaune a Baitlaham bayan fitar da shi daga gidan yarin gwamnatin sahyoniya ya ce: “Sun yi kokarin kashe ni sau da yawa a gidan yarin Ofar, kuma Ben Gvir (ministan tsaron cikin gidan yahudawan sahyoniya mai tsattsauran ra’ayi) na yin rawa a kan gawar tawa yana mai tattake ta!"
Hamas: Ana azabtar da fursunonin mu fiye da na Guantanamo da Abu Gharib
Ubayyat
A cewar cibiyar yada labarai ta Falasdinu Ubayyat ya yi aiki ne a fannin gina jiki kuma ba shi da wata matsala kafin tsare shi, amma a yanzu da kyar ya ke iya motsawa sakamakon mummunar azabtarwa da aka yi masa a gidan yarin gwamnatin sahyoniyawan.
Ubayyat ya bayyana cewa an yi masa mugun duka da azabtarwa a lokacin da ake tsare da shi a karshen watan Oktoban bara.
A karshe dai an sake shi bayan shafe watanni 9 yana tsare a gidan yari na gwamnatin sahyoniyawan, yayin da ya yi asarar nauyi mai yawa na jikinsa kuma ba ya iya motsi.
Ubayyat ya kira gidan yarin Nagib da gidan yarin Guantanamo (inda aka daure shi na wani lokaci agidan yarin), ya ce halin da wannan gidan yari ke ciki ya na kasancewar fursunoni 2000 ke fama da cututtuka masu tsanani da ake tsare da su kuma ake azabtar da su, abu ne da ba za a iya misalta shi ba.