28 Yuni 2024 - 14:26
Ana Ci Gaba Da Kaɗa Kuri'a Zaben Shugaban Ƙasar Iran Karo Na 14 + Hotuna

Wannan zaɓen kamar yadda muka sani ya biyo bayan samuwar hatsarin jirgin sama da aka samu wand ake dauke da shugaban kasar Iran Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi da abokan tafiyarsa wanda suka haɗa da ministan harkokin wajen kasar Iran din.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Tarukan runfuna zaɓen Wanda aka karkafa su a sassan birane da ƙauyukan na kasar Iran sun samu halartar dimbin kwai da kwarkawata na al'ummar kasar Iran daga kuma dukkan sassan al'umma musulumi da wanda ba musulmi ba manyan malamai da ƙanana da jagorori da mabiya addinai daban na kasar suma sun halarci wannan runfuna na zabe don kada kuri'arsu.

Zaben an fara shi tun karfe takwas na safe agogon Iran wanda har yanzu ake gudanar da shi cikin tsaro da shauki na ganin an zabi shugaban mafi inganci wanda zai iya kulawa da al'ummarsa ta ƙasar Iran.

Bugu da kari suma al'ummar Iran wanda suke wajen ƙasar suna ci gaba da Kada kuri'unsu a kasashen da suke zaune a can wasu a Ofisoshin Jakadancin Iran da ke a kasar wasu kuma a wurare da aka kebance su kamar a ƙasar Saudiyya itama ta bayar da wuri don gudanar da wannan zaɓen ga yan kasar Iran.

Wani abun sha'awa da kwanciyar hankali da tsaro shine wasu manyan akwatunan zaben an kafa su ne acikin Manyan masallatai juma'a na kasar dama ƙananan masallaci na Khamsu salwati ind mutane ke ci gaba da kada kuri'arsu cikin aminci da nutsuwa.

Fatanmu ga al'ummar Iran shine Allah Ta'ala ya datar da su wajen zaben shugaba na gari mai inganci da zai kare su da mutuncinsu da tsarin addininsu duniya da lahira.