7 Yuni 2024 - 19:38
Gwamnatin Gaza Ta Bayyana Adadin Alkaluman Kananan Yara Da Gwamnatin Sahyoniya Ta Kashe

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya wallafa yanayin girman laifukan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta aikata kan yaran Gaza ta hanyar fitar da wata sabuwar kididdiga.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Tun bayan fara yakin Gaza sojojin Isra'ila sun shahadantar da fiye da kananan yara Palasdinawa 15,517.

 

Sakamakon wannan yakin sama da yara Palasdinawa dubu 17 ne suka rasa iyayensu daya ko duka biyun.

 

Yara Falasdinawa 3500 ne saboda rashin abinci mai gina jiki ko rashin wadataccen abinci ke kokowa da mutuwa ta dalilin yakin da ake yi. Ya zuwa yanzu, yara Falasdinawa da dama ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki da rashin ruwa.