18 Yuli 2023 - 07:58
Taliban: Damar Gudanar Da Tarukan Muharram Ga 'Yan Shi'a A Duk Yankuna Yana Nan Daram

Kakakin Taliban ya sanar da cewa: batun gudanar da tarukan watan muharran ga 'Yan Shi'a na nan daram, kuma za a gudanar da wandanna tarukan da cikakken matakan tsaro aminci.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, "Zabihullah Mujahid" ya fitar da wata sanarwa tare da sanar da cewa hukumomin tsaron kasar Afghanistan sun dauki cikakken matakan tsaro domin gudanar da tarukan watan Muharram tare da kiyaye 'yancin gudanar da taruka na mazhabar shi'a.

Ya kara da cewa: 'yan uwa mabiya mazhabar shi'a na iya gudanar da taruka da bukukuwan da suka dace da tsarin mazhabarsu a dukkan masaukan da ke yankunansu.