Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Dubban mazauna birnin Tel Aviv, babban birnin gwamnatin sahyoniyawan ne suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matakin da majalisar ministocin wannan gwamnati ta dauka bayan tsige shugaban 'yan sandan Tel Aviv mai cike da cece-kuce.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun rawaito cewa masu zanga-zangar sun tare hanyar Ayalon a birnin Tel Aviv inda suka yi artabu da jami'an 'yan sanda.
Masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa masu tsatsauran ra'ayi a majalisar ministocin Netanyahu sun matsa wa shugaban 'yan sandan Tel Aviv matsin lamba saboda "tsangwama na siyasa" da kuma sassaucin da yake yi wa masu zanga-zangar.
Majiyoyin yaren Ibrananci sun kiyasta adadin mahalarta zanga-zangar na daren jiya a Tel Aviv ina da ya kai mutane 20,000.