Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) ABNA ya ruwaito maku cewa a cikin hadisai da zantukan manyan maluma, an ambace watan Zul-qa’da da girma da siffofi na musamman.
Kamar yadda Sheikh Abbas Qomi ya ruwaito a cikin Mufatihul Janan daga Sayyid Ibn Dawuus, an ruwaito cewa watan Zul Qa’adah wata ne da ake amsa addu’a acikinsa. Daga cikin abubuwan da ake so a yi akwai sallar ranar lahadi a wannan wata, kamar yadda ya zo a hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa, duk wanda ya yi salloli na girmamawa a ranar Lahadin wannan wata, za a karbi tubansa, kuma za a gafarta masa zunubansa, maqiyansa za su yarde masa ranar kiyama, addininsa da imaninsa ba za a kwace masa ba, kabarinsa zaa buda shi da haske, iyayensa su gamsu da shi, gafara zata shafi yanayin mahaifansa da zuriyarsa, zai sami wadatar arziki kuma mala'ikan mutuwa zai yi yi masa da sauki a lokacin mutuwarsa.
Haka nan an ruwaito cewa, duk wanda ya azumci kwanaki uku a jere (da suka hada da Alhamis da Juma'a da Asabar) a daya daga cikin watannin harami, za a rubuta masa ladan ibada na shekara 900.
Ana kuma kiran ranar 23 ga wannan wata ranar ta musamman ga Imam Rida (a.s).
Alamah Majlisi ya bayyana cewa, “Ziyarar Imam Riza, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ita ce mafi falala a ranaku masu tsarki na Musulunci; Musamman kwanakin da aka kebe wa wannan Imami mai Girma” kamar yadda ya zo a hadisi an ambaci ranar 23 ga watan Zul-Qaida a matsayin ranar shahadarsa.
A cikin littafin Ikbal da littafin Taudehil A'amal ranar 23 ga watan Zul-qa’da, Sayyid Ibn Tawus ya ce dangane da Ziyarar Imam Rida (a.s) a wannan rana: “A cikin wasu littafai na wadanda ba Malaman larabawa, na ga cewa ana son yin Ziyarar Imam Rida (a.s) a ranar 23 ga watan Zul-qa'da, daga kusa ko nesa, da daya daga cikin Shahararrun ziyarori ko makamancin haka.
Baya ga abubuwan da aka ambata, bisa lura da riwayar Imam Jawad (a.s) na girman ziyarar mahaifinsa mai girma, yana nuna muhimmancin nuna ladabi da sadaukarwa ga Ali bn Musal Reza (a.s). A yayin da yake bayyana fifikon ziyarar mahaifinsa mai girma da kuma ziyarar Imam Husaini (a.s) Jawadul A'immah (a.s) ya ce: Ziyarar mahaifina ita ce mafi falala, domin dukkan mutane suna ziyartar Sayyidina Aba Abdullah Husain (a.s) Amma ba sa ziyartar mahaifina sai dai kebantattun Yan Shi'a.
Tare da la'akari da kowane dalili (ciki har da ci gaban Imamanci a wajen Imam Rida (a.s) da kuma la'akari da matsayin wilayansa da imamancinsa), ana kiran wannan rana da sunan ranar ziyara Imam Ali Bin Musar Ridha Imami na takwas cikin jerin Imaman Shiriya (a.s) zai karkata zukatan masoya da masu son ziyartar Imam Rida (a.s) zuwa ga wannan limamin.
Dangane da lada da ladan aikin ziyarar Imam Rauf, amincin Allah ya tabbata a gare shi, Akwai ruwayar Ibn Qalawaih Qomi daga Hamdan ta nuna irin girman wannan Ziyarar: Hamdan yana cewa: “Wata rana ina gaban Imam Jawad (a.s) sai na ce: Menene ladan wanda ya ziyarci haramin babanka Sayyidina Ali bin Musar Ridha (a.s) daks Khorasan? Sai Imam ya ce: Duk wanda ya ziyarci kabarin mahaifina, Allah zai gafarta masa zunubansa na baya da na yanzu. Hamdan yana cewa: Bayan haka, sai na hadu da Ayyub bin Nuhu na ce: Na ji haka daga waliyyin Allah Imam Jawad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ayub ya ce: Ba ka so in kara maka ilmi fiye da abin da ka ji? Na ce: Tabbas kuwa inaso. Sai yace: Nima naji wannan ruwaya daga Imam Jawad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sannan ya kara da cewa: “Wadanda suka ziyarci babana ranar kiyama za a dora musu minbari a gaban mimbarin Manzon Allah. Amincin Allah ya tabbata a gare shi, domin dukkansu sun 'yantu daga hisabi da littafin kiyama.
An ambaci ziyarori na Imam Riza (a.s.) a cikin ruwayoyi, amma ziyarar da Sayyid Ibn Tavus ya ruwaito a cikin littafin Al-Ikbal an ambace shi da falalolin wannan Imam wanda shi ne hajji mafi shahara gata nan kamar haka:
اَللّهُمَّ صَلِّ عَلى عَلِىِّ بْنِ مُوسَى الرِّضَا الْمُرْتَضَى الاِمامِ التَّقِىِّ النَّقِىِّ وَحُجَّتِکَ عَلى مَنْ فَوْقَ الاْرضِ وَمَنْ تَحْتَ الثَّرى الصِّدّیقِ الشَّهیدِ صَلوةً کَثیرَةً تآمَّةً زاکِیَةً مُتَواصِلَةً مُتَواتِرَةً مُتَرادِفَةً کَاَفْضَلِ ما صَلَّیْتَ عَلى اَحَدٍ مِنْ اَوْلِیآئِکَ.
Ya Allah ka yi salati ga Ali binu Musar Ridha, imami wanda ya kasance yardadde Imami mai tsantsar takawa da Tsarki wanda yake shine hujjarka akan halittun da suke a doron kasa da wanda suke karkashin kasa, wanda shi shahidi ne mai gaskiya, Cikakken tsarkakakken Aminci mai yawa mai ci gaba da dorewa yana mai bibiyar juna mara yankewa na musamman wanda ya dace sama da yanda kayi aminci ga wani cikin waliyyanka.