Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) - ABNA - ya nakalto cewa: Kamar yadda wakilin Imna ya ruwaito, Ayatullah Muhammad Ali Nasery (1309-S) ya kasance mujtahidi, malamin Akhlak, mai son Imam Zaman (A.S.), wanda shi ne makarantar hauza ta Imam Wali Asr (A.S.) da kuma Cibiyoyin al’adun addini. Suka kasance karkashin jagorancinsa. Ya shafe shekaru da dama yana aikin yada soyayyar Imam Baqiyatullah Al-Azam (AS) a Masallacin Kamrazarin na Isfahan.
Neman Iliminsa:
Sheikh Mohammad ya fara karatunsa ne a Daulat Abad sannan ya ci gaba a makarantar Hauzar Isfahan. Yana dan shekara 14, yayi hijira tare da mahaifinsa zuwa Najaf Ashraf ya. Bayan shekaru uku mahaifinsa ya dawo Iran, shi kuma ya ci gaba da karatunsa a Najaf, inda ya shiga makarantar Sadr da ke birnin Najaf. Kafin ya rabu da dansa mahaifinsa ya fara kai shi ga Amirul Muminina Imam Ali (a.s) sannan kuma ya mika shi ga marigayi Ayatullah Sheikh Muhammad Husain Dehaqani wanda yana daya daga cikin ginshikai kuma jigogi na wannan gari mai alfarma.
A wannan lokacin, ya koyi wani bangare na ilimin adabi inda ya karanta Hashiyar Mulla Abdullah kan nassin hankali na Taftazani da wani bangare na Sharh littafin Lum’ah a wajen marigayi Ayatullah Mudarris Afghani. Inda ya karanta Cigaban littafin Lum’ah a wajen Ayatullah Mujtaba Lankarani, ya karanta littafin Makasab a wajen marigayi Ayatullah Haj Sheikh Abdulkarim Karuni Isfahani, wanda daga baya ya zama sirikinsa. Ya karanta littafin Kifayah a wajen Ayatullah Haj Sheikh Muhammad Hussain Dehaqani, sannan a karo na biyu a gaban Ayatullah Sheikh Sadr, inda ya karanta litafin Badkobehai, da littafin Kharij Salat Ayaat a gaban Ayatullah Sayyid Abdulhadi Shirazi, sanna littfain Kharij Bai’I da Kiyaaarta a gaban Imam Khumaini Qd. Baya ga haka, ya halarci wasu darussa da dama kamar tattaunawa kan littafin Hajji na Ayatullah Sayyid Mahmoud Shahrudi, sannan kuma ya koyi cikakken darasi kan hukunce-hukuncen fikihu a gaban Ayatullahi Haj Sayyid Abulqasim Khui.
Baya ga ilimomi na yau da kullun, ya koyi ilimin ruhintaka daga Mohammad Kufi, Sayyed Muhammad Kashmiri, Sheikh Abbas Quchani, Sayyed Hashem Haddad da Sayyed Jamaluddin Golpayegani. Ya na kuma da masaniya tare da alaka da jiga-jigan sufanci da Halayya irin su Allameh Tabatabaei, Muhammad Ismail Dolabi, Haj Abdul Reza Garda’awi, Maulawi Kandahari. Har ila yau, a mafi yawan tafiye-tafiyensa na wata-wata zuwa birnin Qum ya na isa wajen Ayatullahi Bahjat, kamar yadda Sheikh Ali Agha Bahjat ya ke cewa: Babu wanda ya yi ganawa ta gaske da Ayatullah Bahjat kamarsa.
Ya kamata a ambaci cewa Ayatullah Nasiry da Maulwi Kandahari wanda ba’a san sunansa ba suna da alaka ta 'yan uwantaka a tsakaninsu.
Komawarsa Iran:
Ayatullah Nasiri Daulatabadi ya koma birnin Isfahan ne bisa umarnin malaminsa Ayatullah Sayyid Muhammad Kashmiri, bayan ya koyar da fikihu da Usul da tafsirin kur'ani, wanda ya shafe shekaru da dama yana yi a makarantar hauza ta wannan birni, kuma ya dukufa wajen bayar da horo na tarbiya ga Rayukan mutane da suka shirya domin karbar wadannan ilimomi.
Dalibansa:
Ayatullah Sayyid Abulhasan Mahdawi
Hujjatul Islam Jafar Nasiri
Littafansa:
Ab Hayat: da ya kunshi Tarin lakcocin Ayatullahi Nasiri game da Imam Mahdi (A.S).
Dar Imtidad Nuur: Tarin jawabai da Ayatullahi ya yi game da ayoyin da akayi tawilinsu wa Imam Wali Asr (AS) Imamin karshen zamani.
Rasmu Bandagi: Wannan littafi bayani ne na nassosi daga doguwar hudubar Imam Amirul Muminina (a.s) game da yanayi da dabi'un masu tsoron Allah.
Sukhan Dost: wasu zaɓaɓɓun jawabansa ne game da Kudub Alam Imam Wali Asr (A.S.)
Ayyukkoinsa:
Cibiyoyin addini da ke a biranen Isfahan da Qum da suke karkashin kulawarsa Ayatullah sun hada da:
Makarantar hauza ta Imam Wali Asr (AS)
Makarantar hauza ta Sahib al-Zaman (AS)
Makarantar hauza ta Narjes Khatun (S)
Cibiyar Dijital ta Hazrat Wali Asr (AS) a Daulat Abad
Cibiyar Nazarin Falaki ta Musulunci
Cibiyar Darul Huda Qum
Cibiyar Ilimi Da Sakafa Ta Haadi
Baya ga kokarin ilimi da na addini, Ayatullah Nasiri yana da hannu wajen shiryarwa da shiryar da dalibai da ma'abuta ilimi kan ayyukan alheri. Daga cikin wadannan ayyuka, za mu iya ambaton kokarinsa na kafa cibiyoyin kiwon lafiya da na magani kamar haka:
Cibiyar kula da lafiya ta Sayyid Waliasr (A.S) da sashenta na dialysis na gadaje 20 ya fara ne da taimakon fili mai fadin mita 6,000 da ginin mita 2000 a shekarar 1987 kuma an bude shi a shekarar 1991.
Sashen Dialysis na Asibitin Gladis Shahinshahr
Sashen Dialysis na Asibitin Muhammad Rasuulullah (SAW) Meemah
Dakinn gaggawar marassa lafiya da ke aiki awa 24 a Daulatabad
Allah Ta’ala Yayi Masa Rahamarsa Ya Sadashi Da Annabin Rahama (Sawa) Da Iyalansa Tsarkaka