1 Mayu 2022 - 19:21
Hamas: Za’a Fara Babbar Yaki Da Isra’ila Bayan Ramadan

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Hamas ya bayyana cewa za’a fara yaki babba bayan watan Ramadan, idan har jami’an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da ta’asan da take aikawata a birnin Qudus a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar Hanas Yahyah Sinwar yana fadar haka a wani taro a birnin Gaza a jiya Asabar ya kuma bukaci dukkan dakarun kungiyar su yi shirin shiga yaki babba da yahudawan Isra’ila bayan watan Ramadan, idan har yahudawan sun ci gaba da keta hurumin masallacin al-Aksa .

A cikin makonnin da suka gabata , sau da dama jami’an tsaron HKI sun yi ta keta hurumin masallacin al-aqsa, musamman a lokutan bukukuwan yahudawa. Inda suka korar musulmi masu ibada a cikin masallacin.

Sinwar ya kara da cewa aikin mayakan kungiyar Hamas ne su kare hurumin wurare masu tsarki a kasar Falasdinu da aka mamaye, kuma masallacin alaksa na daga cikinsu.

342/