Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Janar Fenghe, wanda ke tare da rakiyar wata babbar tawagar sojoji zai gana da takwaransa na Iran birigediya Janar Ashtibani.
Zai kuma da wasu manyan jami’an kasar ta Iran, inda zasu tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasa da kasa, yankin da kuma hanyoyin kara hulda tsakanin rundunonin sojoji na kasashen biyu.
Kasashen Sin da Iran dai na da kyakyawar alaka a tsakaninsu da ta hada da tattalin arziki, al’adu da dai sauransu.
342/