24 Afirilu 2022 - 16:50
Yemen Ta Ce; Za Ta Mayar Da Martani Akan Biranen Riyadh Da Abu-Dhabi Saboda Keta Tsagaita Wutar Yaki

Kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Muhammad Abdussalam ya fada a yau Lahadi cewa; A halin yanzu kawancen yakin Saudiyya yana tara runduna a kusa da gundumar Ma’arib, sannan ya kara da cewa; Idan har aka keta shelanta wutar yaki da aka yi, to martanin da zai biyo baya akan biranen Riyadh da Abu Dhabi zai zama mai tsanani.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Abdussalam ya ci gaba da cewa; sojojin kasar Yemen tare da dakarun sa-kai suna cikin shirin ko-ta-kwana domin mayar da martani akan kowane irin wuce gona da iri.

Shi ma Kamfanin man fetur din kasar Yemen ya sanar da cewa; Sauydiyya din tana ci gaba da take shelanta tsagita wuyar yakin ta hanyar ci gaba da rike jirgin ruwa mai dauke da makamashi wanda ya sami amincewar MDD.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Yemen take koken cewa Saudiyya da kawayenta suna ci gaba da kai hare-hare a kasar ba, da hakan yake cin karo da shelanta tsagaita wutar yaki da aka yi a farkon watan nan na azumin Ramadan mai alfarma.

342/