Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Masu Zanga-zangar sun rika bayar da taken nuna goyon bayansu ga masallacin Kudus da al’ummar Palasdinawa da suke fuskantar hare-hare daga ‘yan sahayoniya.
Da safiyar juma’a ne dai sojojin HKI su ka kutsa cikin farfajiyar masallacin kudus inda su ka jikkata palasdinawa da su ka kai 160.
Masu gangamin na Ankara sun kuma yi Allah wadai da yadda kasashen duniya su ka yi shiru akan abinda yake faruwa a Palasdinu.
342/