15 Afirilu 2022 - 14:16
Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Sha Alwashin ci Gaba Da Goyon Bayan Kungiyoyin Dake Fada Da Isra’ila

Wannan bayani ya zo ne a wajen taron tunawa da zagayowar shahadar Brigadier Janar Sayyid Mohammad Hussainzade Hejazi mataimakin kwamandan dakarun kare juyin musulunci na iran da aka yi a ma’aikatar harkokin cikin gida ayau Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Janar Mohammad Zade yayi shahada ne bayan ya jikkata sakamakon harba makami mai guba da aka yi a lokacin yakin kare kasa da aka yi

da yake bayani a wajen taron kwamandan dakarun kare dakarun juyin musulunci na iran brigadier Janar Ghaani ya jaddada matsayinsu na ci gaba da goyon bayan dukkan kungiyoyin gwagwarmayar dake yaki da isra’ila a duniya.

Yace kwanaki 20 da suka gabata dakarun gwagwarmaya falasdinu sun kai hare-hare a birnin telaviv da yankuna daban daban da Isra’ila ta mamaye kan sojojin Isra’ila wanda hakan ke nuna cewa hakurin falasdinawa kan zalunci da Isra’ila ke musu yazo karshe.

342/