Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin wata sanarwa da yan sandan Isra’ila suka fitar sun nuna cewa wani mutum dan shekaru 40 da haihuwa mazaunin garin Khalil dakegabar yammacin kogin jodan ya kai hari kan wani dan sanda da wuka a harabar wani gida dake kusancin garin Ashkelon a yau talata,
Mutum da har yanzu ba’a tantance ko wanene ba ya zaro wuka ne wajen da aka kafa shingayen bincike inda ya cakawa wani jami’in yan sanda dake wurin wanda nan take yan sanda suka harbeshi
Wannan yana zuwa ne kwana daya bayan da kungiyar gwagwarmaya ta hamas tayi kakkausar suka game da kishe-kashen da sojojin Isra’ila suka yi wa falasdinawa a baya bayan nan a yankunan falasdinawa da aka mamaye a yankunan dake gabar yammacin kogin Jodan, wanda hakan ya tona Asirin mummunar aniyar gwamnatin Tel Aviv.
342/