Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Najeriya ce kasa ta 4 dake fitar da iskar gas zuwa Turai inda aka kiyasrta cewa kasha 40 cikin 100 na iskar Gas din da kasar ke fitarwa ana kai shi ne zuwa kasashen Turai.
Tarayyar Turai na son dakatar sayen iskar Gas ne daga Rasha a matsayin mayar da martani kan yakin da ta kaddamar a kan kasar Ukrain, kungiyar tarayyar Turai tana kokarin karfafa dangantaka da Najeriya ne domin samun Karin wuraren da za ta rika sayan iskar Gas da nufin rage dogaro da kasar Rasha
Hukumomin Najeriya sun ce Kasar ta Tabbatar tana da Iskar Gas da ta kai yawan Cubic tiriliyan 209.5 a watan janerun shekara ta 2022 da muke ciki
Daga karshe jakadan kungiyar taryyar Turai a Najeriya Samuel Isopi ya fadi cewa ba suna so mu tsaya a matsayin babbar abokiyar huldar Najeriya ba muna so mu kulla hulda a bangaren sayan isakar gasa saboda mafi yawancin kamfanonin da ake aiki da su na kasashen turai ne.
342/