7 Afirilu 2022 - 12:50
Iran Ta ce Ba Za ta yi Watsi Da Manufofinta Na Nukiliya Saboda Isra’ila Ko barazanar wasu

A wani taron namema labarai da Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya gudanar ya fadi cewa kasar Iran ba za ta ja baya ko kadan ba game da manufofin da take so ta cimma na shirin nukiliya saboda Isra’ila ko kuma barazanar da wasu suke yi mata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau Gwamnatin Isra’ila ta yi kokari samar da takardun bogi da yin zangon kasa a bangaren masana’antu da ayyukan ta’adanci kan kasar iran, amma babu wanda yay yi tir ko ya kalubalanci wannan matakin , wasu ma sun yi maraba das hi ne

Yace shekaru kenan da gwamnatin Isra’ila ta kashe masana ilimin nukiliya na kasar Iran guda 7, kuma ta yi zagon kasa da kai hari kan muhimman Naurorin nukiliyar kasar iran .

Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya suna aiki tare wajen warware damuwar da ake dashi game da ikrarin da hukumar ta yi kan wurare daban-daban a fadin kasar, kuma ana saran nan dan watan yuli mai zuwa damuwar da hukumar take dashi game da wasu wurare 3

Kokarin yin zagon kasa da Isra’ila take yi ne kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya yana zuwa ne adaidai lokacin da ita kanta ta mallaki kayukan makaman nukiliya 200 zywa 400.

342/