Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Takaddamar da ake ayi kan yanakin yammacin sahara na iya zama babbar matsala ga kasar Spain a daidai lokacin da kasashen turai ke neman mafita na samar da iskar gas daga wasu kasashen, bayan takunkumin hana sayar da Gas da aka kakabawa kasar Rasha sakamakon harin da ta kai kasar Ukrain
Wannan matakin yana zuwa ne yan sao’I bayan da kasar Spain ta sanar da nuna goyon bayanta a fili game da shirin kasar Moroko na samun yancin gashin kai a yankin yammacin sahara da ake kai ruwa rana akai , matakin da Spain ta bayyana a matsayin wani sabon yanayi na dangantaka dake tsakaninsu
A shekarar bara ne kasashen Aljeriya da Moroko suka sanar da yanke dangantakar dake tsakaninsu , yayin da kasar Spain da kuma Moroko suna samun rashin jituwa game da batun yan gudun hijira da suka fito daga yammacin Afrika zuwa gabar teku dake yammacin kasar Spain.
342/