Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ana sa bangaren sakatare Janara din Majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres ya fadi cewa wadannan manyan matsaloli guda biyu da ake fuskanta ba zai bari kasar Ukrain ta iya tattara amfanin gona da ta noma ita kuma kasar Rasha tana cikin tsananin takunkumi.
Farashin kayan abinci da man fetur da takin zamani na kara tashin Gwaoron zabi , haka kuma ana samun jinkirin farashin sufuri na shiga da fitar da kaya wanda wannan zai shafi matalauta ne masu karamin karfi kuma zai haifar rashin tsaro da ta siyasa a duniya.
Tuni tasirin haka ya fara bayyana inda dubban Alummar kasar Sudan suka yi zanga-zanga ababban birnin kasar saboda tsadar rayuwa da tashin gwauron zabi na kayan masarufi.
342/