5 Maris 2022 - 20:41
Iran Ta Yi Tir Da Harin Masallacin Peshawar A Pakistan

Iran ta bakin Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi tir da kakkausar murya kan harin ta'addancin da aka kai a ranar Juma'a a masallacin 'yan Shi'a na birnin Peshawar a kasar Pakistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jami'in na Iran ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Juma'a cewa, irin wadannan hare-haren ta'addanci na da nufin haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi.

M. Khatibzadeh ya kuma bayyana bakin cikinsa kan wannan mummunan lamari, tare da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa, Ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Jami'in diflomasiyyar na Iran ya kuma bukaci jami'an tsaron Pakistan da su dauki tsauraran matakai na murkushe 'yan ta'adda don hana sake aukuwar irin wadannan laifuka a nan gaba.

Rahotanni na baya-bayan nan na cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a masallacin na Peshawar ya kai 45, yayin da wasu 65 suka jikkata.

342/