3 Maris 2022 - 17:34
Shugaban Hukumar IAEA Zai Ziyarci Iran Ranar Asabar

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA zai ziyarci Tehran a ranar Asabar mai zuwa domin ganawa da wasu manyan jami'an kasar ta Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bayan tattaunawa mai tsanani a makonnin baya-bayan nan da jami'an Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) suka yi da hukumar ta IAEA da kuma wasu yarjejeniyoyin fahimtar juna da aka cimma, Rafael Grossi zai ziyarci Tehran inda zai ganawa da Mohammad Eslami, shugaban makamashin nukiliya ta Iran AEOI.

Watakila ziyarar ta babban daraktan hukumar ta IAEA a Tehran na da alaka da shirinsa na cimma wata yarjejeniyar hadin gwiwa don warware ‘yar tsarkakiyar dake tsakanin Iran da hukumar ta IAEA.

Mai yiyuwa ne Grossi ya gana da wasu jami'an Iran yayin wannan tafiya.

Rahotanni daga birnin Vienna na cewa, tattaunawar da aka yi tsakanin Iran da hukumar ta IAEA a cikin kwanaki goman da suka gabata tana da sarkakiya da kuma kalubale, amma kulla alaka ta yin hadin gwiwa tsakanin bnagarorin biyu a cikin 'yan kwanakin nan, sun ba da gagarumar gudunmawa wajen ci gaba da tattaunawa.

342/