Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Har ila yau shugaban na kasar Iran ya yi ishara da turjiya da tsayin dakar da kasar Syria ta yi wajen fuskantar ‘ yan ta’adda, sannan ya kara da cewa; Wajibi ne a cigaba da kare iyakokin kasar Syria.
A nashi gefen,Birgediya janar Mamluk ya isar da sakon shugaban kasar Syria, Basshar Asad zuwa ga Shugaban na kasar Iran, yana mai cewa; Babu yadda za a yi gwamnatin Syria ta mance da girman taimakon da Iran ta yi mata wajen fada da ta’addanci da ‘yan ta’adda.
A jiya Litinin ne dai tawagar ta kasar Syria a karkashin jagorancin Birgediya janar Mamaluk ta fara ziyarar aiki, inda bayan ganawa da shugaban kasa, ta kuma gana da ministan harkokin waje da sauran jami’an gwamnati.
342/