Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sojojin HKI sun kai harin ne dai akan wani wuri dake kusa da filin jirgin saman birnin Damascuss.
Sai dai makaman tsaro sararin samaniyar kasar Syria sun kakkabo wasu daga cikin makamai masu linzami da sojojin HKI su ka harba.
Wannan dai shi ne karo na 4 da sojojin HKI su ka kai hari a cikin kasar Syria a wannan watan na Febrairu.
342/