Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka ne a lokacinda yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Venezuela Felix Plasencia Gonzalez, a gifen taron na kasashe masu arzikin iskar gas.
Shugaban ya kara da cewa jajircewar da kasar Venezuela ta yi duk tare da takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dora mata wata babbar alama ce ta turjiyar mutanen wadannan kasashe.
Ya ce: Tare da taimakon mutanen kasar Venezuela kasar za ta farfado daga mummunan halin da ta shiga a shekarun da suka gabata. Raisi ya ce wannan ya nuna mana cewa fada da mamaya da babakere abune mai yuyiwa a wannan zamanin, duk tare da karfin da masu yin haka suke da shi a duniya. A na shi bangaren ministan harkokin wajen kasar Venezuela ya ce kasarsa tana son karfafa dangantakka da kasar Iran a dukkan fagage.
342/