Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Ministan tsaron kasar ta Rasha Sergie Shoigu ya jagoranci wata tawagar soja ce zuwa Syria domin duba wani atisayen soja da jiragen ruwan kasarsa suke yi a sansaninsu na Tartus.
Bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin fadada alaka a tsakaninsu da suka hada da fada da ta’addanci.
Shoigu ya jaddada cewa;kasarsa za ta ci gaba da aiki tare da kasar Syria ta fuskar aikin soja, musamman ma a fagen fada da ayyukan ta’addanci.
342/