31 Janairu 2022 - 19:27
kasashen Iran Da Faransa Sun Bukaci Daukar Matakai Masu Tasiri A Tattaunawar Vienna

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta gudana tsakanin shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi da takwaransa na kasar Fransa Emanuel Macron ta tsawon sa’a daya, sun bukaci a ci gaba da tattaunawa tsakanin kasashen biyu da zimma zurfafa dangantaka dake tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - D ayake amsa tambayar da manema labarai sukai masa kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatib Zade ya fadi cewa dangantaka tsakanin Tehran da Paris a bangarorin daban daban zai yi tasiri sosai wa shawarwar da za’a yanke a tattaunawar da ake yi kan nukiliyar iran da cire mata takunkumi

Yace Iran tana kare matsayinta ne a tattaunawar a afili, kuma tattaunawar da shuwagabannin kasashen biyu suka yi za ta yi tasiri sosai wajen shawarar da za’a yanke a wajen tattaunawar Vieanna.

342/