20 Janairu 2022 - 10:01
Sudan:Mutane Sun Toshe Manya-Manyan Tituna Don Nuna Fushi Na Kissan Masu Zanga-Zanga

Fararen hula masu zanga-zangar kin jinin sojoji masu juyin mulki a kasar Sudan sun tottoshe manya-manyan tituna, tare da kona tayoyi don nuna rashin amincewarsu da kissan masu zanga-zanga wanda sojojin suka yi a ranar litinin da ta gabata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ ya bayyana cewa a ranar Litinin ne sojojin kasar ta Sudan masu juyin mulki suka bude wuta kan masu zanga-zanga, inda suka kashe akalla mutane 7, daga ciki har da wani sanennen dan kasuwa wanda ake kira Usman El-Sharif.

A ranar 25 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ce sojojin kasar ta Sudan suka kawo karshen gwamnatin rikon kwarya wacce aka dorawa nauyin gudanar da zabubbuka don maida kasar kan turbar Democradiyya a wani juyin mulkin da ba’a zubar da jini ba.

Amma jam’iyyun siyasa da kuma kungiyoyin fararen hula sun ki amincewa da juyin mulkin kuma tun lokacin ne suke fitowa kan tituna cikin lumana don nuna rashin amincewarsu da juyin mulkin.

342/