18 Janairu 2022 - 13:54
​Masar Da Aljeriya Sun Tattauna Game Da Batun Libiya

Kasashen Masar da Aljeriya sun tattauna a tsakaninsu game da batun sanya baki na kasaashen ketara a harkokin cikin gidan kasar Libiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bangarorin sun tattauna ne yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Aljeriya Ramtane Lamamra ya kai a birnin Alkahira na kasar Masar, inda ya gana da takwransa na Masar Sameh Choukri.

Kasashen biyu sun amince da kawo karshen duk wani shishigi a harkokin cikin gidan Libiya, da kuma kwashe dukkan mayaka da sojojin haya na kasashen ketare a kasar ta Libiya.

Haka zalika bangarorin sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi alakar dake tsakaninsu.

Sun kuma kudiri anniyar zurfaffa alakarsu a bangarori daban daban, musamman tattalin arziki da kuma zuba jari.

A daya bangaren kuma sun tattauna kan halin da ake ciki a kasashen Sudan, Mali, da kuma yankin sahel da kuma sahara, inda suka bayyana wajabcin karfafa hadin guiwa ta tsakanin kasashen afrika, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da kwanciyar hankali duba da halin da ale ciki a yankin.

342/