Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Iyalan mamacin sun fadi cewa tsaohon shugaban kasar ta mali Ibrahim bubakar kaita da ya jagoranci kasar daga shekara ta 2013 zuwa 2020 ya mutu ne da misalinin karfe 9 na safe agogon mali a gidansa dake birnin Bamako fadar mulkin kasar,
An zabi Ibrahim bubkar kaita ne a shekara ta 2013 kuma sojojin sun kifar da gwamnatinsa ne a watan Agustan shekara ta 2020.
Wannna sanarwar ta zo ne adaidai lokacin da fira ministan kasar ya sanar da cewa za su shigar da kokensu a hukumance na kalubalantar takunkumin da kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afrika Ecowas da kuma kungiyar kula da kudade ta yammacin afirka ta kakaba mata.
342/