11 Janairu 2022 - 14:34
​An Kama Wani Dan Leken Asirin Isra'ila A Zirin Gaza

An kama wani dan leken asiri na Mossad wanda ya kashe wani masanin kimiyar Falasdinu a Malaysia a shekarar 2018.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kafofin yada labaran Falastinu sun bayar da rahoton cewa, Jami’an tsaro Gaza sun kama wani jami’in kungiyar Mossad kuma wanda ya aikata kisan gillar da aka yiwa wani masanin kimiya na Falasdinu a Malaysia a shekarar 2018.

A ranar 21 ga Afrilu, 2018, wannan mutumin ya kashe wani masanin kimiya na Falasdinu, Mohammad Al-Batash a Malaysia ta hanyar harbinsa da harsashi 10.

Ikirari da ya yi kan kisan, ya nuna cewa an aiwatar da aikin da aka ambata bisa umarnin Mossad ne.

Fadi al-Batash yana da shekaru 35 jigo nea kungiyar Hamas kuma mazaunin yankin Jabalya da ke Gaza, wanda jami’an leken asirin yahudawan suka yi hankoron kashe shi a lokuta daban-daban, kafin kashe shi da suka yia Malaysia.

Shekaru biyu da suka gabata shugaban hukumar leken asiri ta Isra'ila Mossad ya amince cewa 'yan leken asirin gwamnatin Isra’ila sun kashe wasu shugabannin kungiyar Hamas a kasashen waje.

342/