10 Janairu 2022 - 15:04
ECOWAS Ta Yanke Hulda Da Mali Ta Kakaba Mata Takunkuman Tattalin Arziki Mafi Tsanani

Kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta yanke huldar jakadanci da Bamako ta kuma rufe duk kan iyakokinta da kasar ta sama da kasa saboda sabawa wa’adin da gwamnatin sojojin kasar ta yi na gudanar da zabubbuka a cikin wannan shekara ta 2022, maimakon haka ta maida shi zuwa shekara ta 2025.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - bayyana cewa kungiyar mai kasashen 15 ta dauki wannan matakin ne a jiya Lahadi a wani taro na musamman da kasashen suka gudanar a birnin Accra na kasar Ghana.

A jawabin bayan taron da kasashen suka bayar ya kara da cewa, kungiyar ba zata amincewa sojojin kasar su maida mutanen Mali a matsayin garkuwa don ci gaba da shugabancin kasar ba.

A tana bangaren gwamnatin sojojin kasar ta Mali ta bayyana cewa ta kadu sosai da jin wannan mataki mai tsananin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan kasar, kuma ta yi allawadai da daukar wannan matakin a kanta.

Kakakin gwamnatin kasar ta Mali Abdoulaye Maiga ne ya maida wannan martanin a safiyar yau Litinin ya kuma kara da cewa gwamnatinsa ta dauki matakin dage zaben ne saboda matsalolin tsaron da kasar take fama da su.

Shugaban kasar ta Mali Assimi Goita ne ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Abubakar Kaita a cikin watan Augustan shekara ta 2020, sannan ya sake jagorantar wani juyin mulkin a cikin watan Mayu shekara ta 2021.

342/