9 Janairu 2022 - 15:50
Bakar kiyayyar Da Amurka Ke Nunawa Iran Saboda Riko Da Addini Da Alummarta ke yi ne

Jagoran juyin Musulunci na Iran Ayatullah Imam Khamina’I ya fadi hakan ne asa’ilin da yake jawabi game da zagayowar ranar yunkurin mutanen Qum na kalubalantar tsohuwar gwamnati sarki sha mai samun goyon bayan Amurka a ranar 9 ga watan janerun shekara ta 1979 .

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jagoran ya saba karbar bakunci dubun dubatan mutanen Qum a duk irin wannan rana ,sai dai a wannan karon yayi wa alumma jawabi ne sa ta gidan talbijin saboda matsalar Annobar Korona.

Ana daukar yunkurin 9 ga watan janerun shekara ta 1979 mai matukar muhimmanci a tarihi, kuma sharar fage na ya yaduwar zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin shah a sassan kasar,wadda ta girgiza gwamnati Shah da ya kai ga cin nasarar juyin musulunci a shekara ta 1979

Masharhanta na danganta yunkurin 9 ga watan janeru a matsayin dan ba na cin nasarar juyin juya halin musulunci a kasar iran da marigayi Imam Khumaini ya jagoranta.

342/