Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara sunayen mutane 51 cikin jirin suneyen jami’an gwamnatin Amurka da kuma kwamandoji wadanda suke ha hannun wajen taimakawa ayyukan ta’addancin a duniya ta hanyar kashe Sulaimani.
A ranar 3 ga watan Jenerun shekara ta 2020 ne tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada umurnin kissan Janar Sulaimani a tashar jiragen sama na birnin Bagdaza a kasar Iraki.
Banda haka Iran ta bukaci kwamatin tsaro na MDD ya dauki gwamnatin kasar Amurka a matsayin gwamnati wacce take goyon bayan ayyukan ta’addanci a duniya.
A cikin jerin sunayen jami’an gwamnatin kasar ta Amurka wadanda suka shiga bakar littafi na kasar Iran dai sun hada da tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump, sakataren harkokin wajensa Mike Pompeo, mai bawa gwamnatinsa shawara kan harkokin tsaro John Bolton, Mark Esper, Gina Haspel, Christopher Miller da Steven Mnuchin.
342/